…Masu garkuwar sun kafa sansani a Jihar Neja
Mutanen da ke gudun hijira saboda hare-haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a kananan hukomomin Shiroro da Rafi sun ce wasu lokuta a daji suke kwana, saboda addabarsu da ake yi. ’Yan bindigar na matukar tada zaune-tsaye a yankunan a ’yan watannin nan, inda a kwanakin baya suka kai hari a kauyuka 12 […]
Mutanen da ke gudun hijira saboda hare-haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a kananan hukomomin Shiroro da Rafi sun ce wasu lokuta a daji suke kwana, saboda addabarsu da ake yi.
’Yan bindigar na matukar tada zaune-tsaye a yankunan a ’yan watannin nan, inda a kwanakin baya suka kai hari a kauyuka 12 a kananan hukomomin biyu, inda suka kashe mutum 13 suka raunata da dama.
Haka kuma ’yan bindiyar sun yi garkuwa da Hakimin Madaka Alhaji Zakari Ya’u da matarsa da Dagacin Kukoki da wadansu mutum hudu, wadansu kuma suka gudu daga kauyen.
Harin ya tursasa sama da mutum 5000 barin gidajensu, inda wadansu daga cikinsu suka koma wasu sansanonin gudun hijira a Kagara da Rafi da Kuta da Gudu a Karamar Hukumar Shiroro.
A sansanin Kuta, wani mai suna Sulaiman Nagogo ya bayyana yadda ’yan bindigar suka kashe masa jikoki, “Yanzu haka a daji muke barci, sannan sai mu shiga cikin gari da safe domin Sallah da neman abinci. A ranar wata Asabar, mun idar da Sallar Asuba ke nan sai muka ji babura suna shigowa, kuma sai muka fara jin harbin bindiga. Muka fara gudu, sai jikokina biyu suka shiga wani gida, inda ’yan bindigar suka bi su ciki suka jawo su waje. A nan suka tilasta wa irinmu da muka kasa guduwa kallon yadda suka yanka su kamar dabbobi,” inji shi.
Ya ce shugaban ’yan bangar garin, Malam Ahmadu Ladan shi ma haka ’yan bindigar suka yi masa, wanda hakan ya sa matarsa ta yanke jiki ta fadi kuma har yanzu take asibiti.
Nagogo ya ce wannan ne ya sa mutanen yankunan suka gwammace kwana a cikin daji, “Suna kawo hari duk lokacin da suka ga dama. Muna ganinsu suna yawo a kan babura, kuma da alama ba su da ranar bari, shi ya sa muka bar musu garin,” inji shi.
Hakimin Gurmana, Alhaji Aliyu Umar ya bayyana wa manema labarai cewa mutanensa da dama ciki har da mata masu shayarwa da kananan yara suna kwana a cikin daji, sannan da yawa ba a san inda suke ba.
“Abin da zan ce shi ne ina rokon Gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello ya kawo mana dauki,” inji Hakimin.
A Babbar Makarantar Firamare ta Kagara, Isah Salau ya ce ya rasa ’ya’yan wansa biyu da suke wajensa, sannan Makama Aminu shi ma ya rasa ’yan uwa 10 a cikin wata uku da suka gabata.
Galadiman Kagara, Alhaji Abdullahi Usman Kateko da Walin Kagara Alhaji Shehu Ibrahim Kajawa dukan mutanen Karamar Hukumar Rafi, sun yi gargadin cewa ’yan bindigar na neman hada wata daba a yankin.
“Masu garkuwa da mutanen na neman hada daba a yankin nan domin akwai babban daji mai girma da zai ishe su kamar Sambisa a Jihar Borno. Kuma hakan ya jefa tsoro a zukatan mutane. Domin haka ne babu yake son komawa yankin. Mutanen nan yawancinsu manoma ne, kuma suna bukatar komawa gona. Wannan dajin da muke magana shi ne ya yi ta Pandogari. Mun dade muna kira ga Gwamnatin Tarayya ta ajiye sojoji a tsakanin kananan hukomomin nan biyu,” inji shi.
Ya ce, “Yankunan da suka kwace suna da yawa, kuma suna neman kwace wasu.”
A daidai lokacin da ake jimamin matsalolin tsaro a Jihar Neja, sai kwatsam ’yan bindiga suka sace wadansu ’yan kasashen waje guda biyu da wadansu mutum shida a Karamar Hukumar Shiroro.