Masu goyon bayan Rasha da Tarayyar Turai sun yi karon-batta a Ukraine
Masu zanga-zangar da ke goyon bayan kasar Rasha da masu adawa da ita sun yi karo da juna a yankin Crimea da ke kasar Ukraine, bayan faduwar gwamnatin kasar, karkashin tsohon shugaba biktor Yanukobich.Dubban masu zanga-zanga da ke goyon bayan Rasha sun fafata da masu goyomn bayan sabuwar gwamnatin da aka kafa a kasar.Kimanin mutum […]

Masu zanga-zangar da ke goyon bayan kasar Rasha da masu adawa da ita sun yi karo da juna a yankin Crimea da ke kasar Ukraine, bayan faduwar gwamnatin kasar, karkashin tsohon shugaba biktor Yanukobich.
Dubban masu zanga-zanga da ke goyon bayan Rasha sun fafata da masu goyomn bayan sabuwar gwamnatin da aka kafa a kasar.
Kimanin mutum dubu biyu ne, ’yan kabilar Tatar da ke zaune a gabar tekun Black Sea, suka yi taron goyon bayan kungiyar ‘Euromaidan’ wadda ta yi fafutikar kawar da mulkin Yanukobich a babban binin kasar Kieb, bayan da ta shafe watanni uku tana gudanar da zanga-zanga. A kan hanyar su suka ci karo da tamkarsu, wadanda ke goyon bayan Rasha a wajen majalisar Crimea, kuma suk yi da tur da wadanda suka kwace mulki a babban birnin kasar.
’Yan sanda sun yi kokarin shiga tsakanin bangarorin wadanda ba su ga maciji da juna. Wannan yanki na Crimea ya koma cikin Ukraine daga kasar Rasha a shekarar 1954, a zamanin mulkin shugasban Rasha Nikita Khrushche. ballewar wannan yanki. Da rashin goyon bayansa ga sabuwar gwamnatin kasar na iya haifar da rikicin raba kasa, kamar yadda masu bibiyar nazarin rikicin siyasar da tya baibaye Ukraine ke ta ce ce ku ce a kai.
Tun bayan faduwar Gwamnatin Yanukobich, idon duniya ya koma kan Shugaba Putin na Rasha, wanda a shekarar 2008, ya bayar da umarnin mamaye kasar Georgia, don gudun kada sasuran yankunan Abkhazia da Kudancin Ossetia, inda mafi yawancin kabilun Rasha, kuma a karshe ya saduda ya kyale su suka karbi ’yancin kansu. Wannan rikicin siyasa da ya addabi kasar Ukraine ya yi kamari ne, bayan da aka sako tsohuwar Firayiministar kasar, Yulia Tamashenko, wadda aka daureta shekara biyu da suka gabata, bisa tuhumar cin hanci da rashawa.
Manyan kasashen duniya, wadanda suka hada da Amurka da Birtaniya sun gargadi Rasha kada ta mamaye kasar, amma tuni Shugaba Putin ya bai wa rundunar sojojin ruwa da na kasa da na sama da su zauna cikin shirin ko ta kwana.