Masu gurasa sun fara yajin aiki a Kano
Masu gurasa sun koka cewa tsadar kayan hadi na barazana ga sana’ar.
Masu gurasa a Jihar Kano sun fara yajin aikin gargadi saboda barazanar da sana’ar ke fuskanta sakamakon tsadar fulawa.
Kungiyar Masu Gasa Gurasa a Jihar Kano, ta ce yajin aikin na wuni uku ya zama dole duba da tashin gwaron zabon da farashin fulawa ya yi, wanda ya sa masu sana’ar shiga cikin halin ni ’yasu.
- Yadda ’yan bindiga ke cin karensu ba babbaka a Zariya
- Shin da gaske baraka ta kunno kai tsakanin Buhari da Tinubu?
Shugabar Kungiyar, Amina Abubakar, ta ce “Mun dade muna ta surutu kan tashin farashin fulawar, kullum ka je sayen fulawar sai ka ji farashinta ya tashi.
“Yanzu dai tura ta kai bango. A bangon ma mun kume don haka ba za mu iya ci gaba da gudanar da sana’ar a wannan yanayin ba,” inji shugabar.
Ta ce duk da cewar masu sana’ar za su iya shiga wani hali, amma hakan shi ne kadai matakin da ya rage musu don nuna halin da suke ciki.
Malama Amina ta ce masu gurasar sun dade suna kokawa game da rashin tsayayyen farashin gurasa amma sun rasa mai sauraren su.
“Idan kin duba yawancin masu yin gurasa mata ne iyayen marayu. Sai mun yi gurasar nan muke iya ciyar da iyalinmu.
“Amma mun dogara ga Allah. A gaskiya muna cikin halin da muke bukatar taimakon gwamnatin a sana’armu.
“A yanzu da yawa daga cikinmu an daina ba su bashin fulawar, yayin da wadansu kuma an daure su a gidan gyaran hali.
“Ita gurasa Allah Ne kadai Ya san mutane da ke ci a cikinta. Za mu yi gurasa a nan mai fulawa da mai sayar da itace ko kara ya samu.
“Yara su dauko mana itace da ruwa mu biya su lada. Sannan idan an gama masu talla su dauka su fita da ita wurare daban-daban don sayarwa.
“Allah Ne Ya san garuruwan da ake kai gurasar nan a kullum.
“Gurasar nan ana kai ta abbatuwa, a nan mai tsire zai saya, mai balangu zai saya. Kai in takaice muku masu sayar da takardar nama ma sai sun ji a jikinsu,” inji ta.
Shugabar ta yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da mai dakinsa Hafsat da su taimaka musu don ganin sun samu saukin farashin gurasar don ci gaban sana’arsu.