Masu haddasa rikicin addini ba addinin ne manufarsu ba – Imam Bunza
Wani fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Kebbi Imam Hali Bunza ya ce masu kokarin haifar da rikici a tsakanin Musulmi da Kirista ba addini ne ya dame su ba sai dai suna yin haka ne don karkata hankulan ’yan kasa yayin da su kuma za su yi ta sace arzikin kasar don kansu.Malamin ya […]
Wani fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Kebbi Imam Hali Bunza ya ce masu kokarin haifar da rikici a tsakanin Musulmi da Kirista ba addini ne ya dame su ba sai dai suna yin haka ne don karkata hankulan ’yan kasa yayin da su kuma za su yi ta sace arzikin kasar don kansu.
Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke zantawa da Aminiya bayan kammala Sallar Juma’ar makon jiya a garin Bunza, inda ya ce, “Mu sani fa Allah ne Ya yi mu kuma Ya hada mu zama tare a wannan kasa kuma ya yi mu kabilu daban-daban ba tare da ba mu zabi ba. Kuma Ya yi haka ne don mu fahimci juna ba don mu yi fada da juna ba.”
Ya nuna takaici kan yadda wasu mutane ke ta kisan bayin Allah ba tare da sun yi laifin komai ba, kamar su Sheikh Jafar da kuma Sheikh Albani a baya-bayan nan, “Kuma tabbas Allah ba zai bar duk wanda ke da hannu a kisan su ya zauna lafiya ba,” inji shi. Ya bukaci hukuma ta zakulo makasan wadannan bayin Allah don a yi musu hukunci.