Masu hannun jari sun samu Naira biliyan 264
Aminiya ta gano cewa masu hannun jari a kamfanoni 22 sun samu Naira biliyan 231 yayin da kamfanonin suka biya su jarin da suka sanya bayan karewar shekarar 2017. Wadanda suka fi samun kudi su ne masu hannun jari a kamfanin siminti na Dangote wadanda suka samu Naira 10 da kwabo 50 a kowane […]
Aminiya ta gano cewa masu hannun jari a kamfanoni 22 sun samu Naira biliyan 231 yayin da kamfanonin suka biya su jarin da suka sanya bayan karewar shekarar 2017.
Wadanda suka fi samun kudi su ne masu hannun jari a kamfanin siminti na Dangote wadanda suka samu Naira 10 da kwabo 50 a kowane hannun jari na Naira biliyan 17 wadanda suka kai Naira biliyan 179.
Kamfanin sarrafa abinci na Nestle ya bayar da Naira 42 da kwabo 50 a kowane hannun jari ga daukacin miliyoyin masu hannun jari inda hakan ya kai Naira biliyan 33 da digo shida wanda ya kai kashi 12 da digo takwas cikin dari.