Masu harkar PoS sun yi cinikin tiriliyan N15 a shekara 2 a Najeriya

A shekara guda an yi hadahadar tiriliyan N8.92 kuma rumfunan PoS sun karu karu zuwa miliyan 2.164.

Masu harkar PoS sun yi cinikin tiriliyan N15 a shekara 2 a Najeriya

Injin POS

Cinikin da masu rumfunan hadahadar kudade na PoS a Najeriya suka yi ya kai na Naira tiriliyan 15 da biliyan 465 a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Rahoton kamfanin tura kudade na Inter-Bank Settlement ya nuna a daga watan Satumban 2021 zuwa Satumbar bana, an yi hadahadar Naira tiriliyan 8.92 kuma yawan rumfunan ya karu karu zuwa miliyan 2.164, daga miliyan 1.104 da ake da su a 2021.

Rahoton ya ce, a daga watan Satumban 2020 zuwa 2021 kuma an yi hadahadar Naira tiriliyan 6.54 a hadahada miliyan 2.14 — jimilla Naira tiriliyan 15.465.

Ya bayyane cewa zuwa watan Satumban 2021, cibiyoyin POS da da ke Najeriya sun karu zuwa miliyan 2.164 daga miliyan 1.104 da ake da su a 2021.

Dalilin karuwar harkar PoS a Najeriya

Da yake karin haske ka lamarin, Mataimakin Shugaban Cibiyar Kasuwanci da Masana’atu ta Legas (LCCI), Gabriel Idahosa, ya alakanta bunkasar hadahadar POS a Najeriya da karuwar masu shiga harkar da kuma karfin kasuwanci.

Ya ce “Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba da izi ga  masu harkar, irin su Momo Money daga MTN da Smart Cash na Airtel,” in ji shi.

Sannan karuwar kamfanonin kasuwanci ta hanyar fasahar zamani da kuma amfani da fasahar wajen wayar da kan jama’a kan hakar sun taimaka.

“An samu karuwar kamfanonin kasuwanci ta fasahar zamani da ke tallata harkar, sannan kamfanonin ma’aikatu sun rungumi amfani da ita.

“Yanzu hukumomin gwamnati da kamfanonin wutar lantarki da makarantu sun amince suna amfani da tsarin PoS; sannan bankuna sun tashi wurjanjan wajen tallata harkar ta PoS,” in ji Idahosa.

Ya ce bayan haka, tasirin cutar COVID-19 da tsarin gwamnati na rashin daukar takardun kudi su ma sun taimaka wajen bunkasar harkar PoS.