Masu ilimin addini suka dace da shugabanci– Malam Nuhu Kayarda

Aminiya: Yaya kake ganin tafiyar kananan hukumomin kasar nan, musamman daga lokacin da aka dawo mulkin dimokurdiyya zuwa yanzu?Malam Nuhu Kayarda: Wato gaskiyar magana kananan hukumomin kasar nan, suna cikin mawuyacin hali, daga lokacin da aka dawo mulkin dimokuradiyya zuwa wannan lokaci da muke ciki.  Domin tunda aka dawo mulkin dimokuradiyya ana yin mulki ne […]

Masu ilimin addini suka dace da shugabanci– Malam Nuhu Kayarda
Masu ilimin addini suka dace da shugabanci– Malam Nuhu Kayarda

Aminiya: Yaya kake ganin tafiyar kananan hukumomin kasar nan, musamman daga lokacin da aka dawo mulkin dimokurdiyya zuwa yanzu?
Malam Nuhu Kayarda: Wato gaskiyar magana kananan hukumomin kasar nan, suna cikin mawuyacin hali, daga lokacin da aka dawo mulkin dimokuradiyya zuwa wannan lokaci da muke ciki.  Domin tunda aka dawo mulkin dimokuradiyya ana yin mulki ne kamar na soja, ba a bai wa al’umma dama su zabi shugabannin da suka dace. Don haka duk kudin da ake turo wa kananan hukumomi daga Asusun Tarayya, domin a gina asibitoci da hanyoyin mota da makarantu da inganta harkokin noma duk ba a ganin komai, al’umma ba su amfana da komai. Saboda haka muna kira ga wannan gwamnati ta Shugaban kasa Muhammad Buhari kan a bai wa kanannan hukumomi ’yancin cin gashin kansu, domin shi ne zai magance wannan danniya da ake yi musu.
Aminiya: Me ya karfafa maka gwiwar fitowa takarar nemanshugabancin karamar Hukumar Lere?
Malam Nuhu Kayarda: Wato tunda nake ban taba neman wani shugabanci ba, sai dai in shugabanci ya zo gare ni na kan karba. Dalilin da ya sa na fito wannan takara shi ne shugabannin wannan jam’iyya tamu ta APC ta mazabar Kayarda ne, suka bukaci in fito takara. Domin suna ganin idan Allah Ya sa aka zabe ni, akwai gudunmawar da zan bayar wajen ci gaban karamar hukumar. Kuma tunda na fito takara zuwa yanzu al’ummar karamar hukuma sun rungume ni hannu bibbiyu. Amma duk da haka ina neman zabi wajen Allah kan wannan takara da na fito.
Aminiya: Idan aka samu nasara wadanne kudirori kake da su kan karamar hukumar?
Malam Nuhu Kayarda: Babban kudirina ga karamar hukumar idan Allah Ya sa na samu nasara shi ne in yi abin da Allah Ya yi umarni ga shugaba ya yi wa al’ummar da yake shugabanta. Duk wani abu da yake hakki ne a yi wa al’umma zan yi iyakar kokarina wajen sauke wannan hakki. Duk wata dukiya ta wannan karamar hukuma da aka bayar aka ce a yi wa al’ummar karamar hukumar aiki, zan yi iyakar kokarina wajen ganin na yi haka. Domin amana ce Allah Ya ba ni, idan na ha’inci al’ummar wannan karamar hukuma Allah ba zai bar ni ba. Domin na san idan ban yi adalci ba, Allah zai tambaye ni ba zai bar ni ba. Manzon Allah (SAW) ya ce kowane shugaba a ranar tashin Alkiyama, zai zo hannunsa a daure adalcin da ya yi wa al’ummarsa ne zai kwance shi. Don haka ina rokon Allah idan Ya sa na samu nasara, in yi adalci kamar yadda shugabanninmu na farko irin su Ahmadu Bello da Tafawa balewa suka yi. Duk shugabannin da ba su yi adalci kan shugabancin da aka ba su ba, Allah zai sa jama’a su manta da su kuma za su ga abin da suka yi. Don haka za ka ga shugabannin sun yi shugabanci sun saci dukiyar jama’a amma suna sauka, sai a nemi dukiyar a rasa saboda ba dukiyarsu ba ce, dukiyar al’umma ce.
Aminiya: Ba ka ganin wasu za su yi mamakin fitowarka takara, ganin kai malamin addini ne?
Malam Nuhu Kayarda: Zai iya zamantowa abin mamaki kuma zai iya zamantowa ba abin mamaki ba. Domin kamar yadda ka fada ni shugaba ne na kungiyar addinin Musulunci a wannan karamar hukuma, kuma an ba ni wannan shugabanci ne don in gabatar da abin da ake bukata ga al’umma. Ita ma wannan takara da na fito abu ne da ya shafi al’umma baki daya. Don haka tunda ina shugabancin al’umma a wata kungiya, kuma yanzu na zo ina son in shugabanci al’umma baki daya babu wani abin mamaki. Domin ai abin da ake bukata ke nan. Ba ka’ida ba ce a bar shugabancin al’umma ga wadanda ba su da iilimin addini. Domin idan aka ce shugaba ba ya da ilimin addini, ta yaya zai tafiyar da shugabancin al’umma ya yi masu abin da suke so? Ta yaya tsoron Allah zai kama shi, idan aka kawo masa hakkokin jama’a? Ya kamata duk wanda za a zaba kan wata kujera a Najeriya ya kasance yana da ilimin addini. Domin da ilimin addinin Musulunci da ilimin addinin Kirista dukkansu suna koyar da tsoron Allah ne da yin adalci. A yau idan aka ce a Najeriya shugabannin wadannan addinai biyu ne suke shugabanci ba za a samu matsala ba. Domin shugabanci ba ya yiwuwa yadda ya kamata, sai da ilimin addini. Ba maganar ilimin zamani ba ne shugabantar jama’a, ilimin zamani ana amfani da shi ne wajen aiwatar da al’amura, amma ba a samun damar a yi adalci da abin da ake bukata, sai da ilimin addini. Ilimin zamani ba tsoron Allah yake koyarwa ba, amma ilimin addini yana koyar da tsoron Allah da sanin hakkokin jama’a. Don haka idan ba ka da ilimin addini yaya za a yi ka ji tsoron Allah tare da gabatar wa al’umma hakkokinsu? Wannan shi ne yake kawo mana matsalar rashin adalci a tsakanin shugabanni a Najeriya, tun daga matakan kananan hukumomi da jihohi har zuwa tarayya. Duk shugaban da yake da ilimin addini koda ya yi ba daidai ba, ya sani kuma ya san Allah ba zai bar shi ba, amma shugaban da ba ya da ilimin addini, zai ga babu wata matsala domin bai sani ba.
Aminiya: Bisa ga dukkan alamu nan ba da dadewa ba za a gudanar da zaben kananan hukumomi, wace kira ko jan hankali za ka yi ga shugabannin jam’iyyarku ta APC, game da zabo wadanda suka cancanta don tsayawa takara a wannan zabe?
Malam Nuhu Kayarda: To, ina ba da shawara ga shugabannin jam’iyyarmu ta APC su tsaya su zabi mutanen da suka dace don tsayar da su takara a zaben kananan hukumomi. Su tabbatar duk wanda za su tsayar takara ya kasance mutum ne nagari, wanda zai yi wa al’umma aiki tare da kawo ci gaba a karamar hukumarsa. Domin gaskiyar magana a baya shugabannin jam’iyyu ba su rika tsayar da mutanen da suka dace ba a takarar shugabancin kananan hukumomi a Najeriya ba, don haka aka yi ta samun matsaloli. Saboda haka muna fatar shugabannin jam’iyyarmu ta APC za su yi gyara kan wadannan matsaloli da aka samu a baya.
Aminiya: A karshe mene ne sakonka ga al’ummar karamar Hukumar Lere?
Malam Nuhu Kayarda: Sakona ga al’ummar karamar Hukumar Lere shi ne su ci gaba da addu’ar Allah Ya zabar musu shugaban karamar hukuma nagari mai adalci wanda zai kawo masu alheri. Haka kuma ina kira ga shugabannin jam’iyyarmu ta APC na wannan karamar hukuma su ji tsoron Allah su  tsayar da mutumin da ya cancanta.