Masu jayayya da shugabannin APC su bari a ceto kasar nan – Yusha’u Kebbe
Yusha’u Ahmad Kebbe dan takarar Gwamnan ne a tsohuwar Jam’iyyar ANPP da ya kara da Gwamna Wamakko a zaben da ya gabata kuma yanzu dan Jam’iyyar APC ne, ya tattauna da manema labarai kan harkokin jam’iyyarsa ta APC da abubuwan da suka shafi siyasa da tsakaninsa da ubangidansa na siyasa wato Alhaji Attahiru Bafarawa da […]
Yusha’u Ahmad Kebbe dan takarar Gwamnan ne a tsohuwar Jam’iyyar ANPP da ya kara da Gwamna Wamakko a zaben da ya gabata kuma yanzu dan Jam’iyyar APC ne, ya tattauna da manema labarai kan harkokin jam’iyyarsa ta APC da abubuwan da suka shafi siyasa da tsakaninsa da ubangidansa na siyasa wato Alhaji Attahiru Bafarawa da dangantakarsa da Wamakko da sauransu.
Aminiya: Mene ne makasudin ziyarar da ka kawo wa manema labarai a cibiyarsu ta Sakkwato?
Kebbe: Na kawo wannan ziyara ce domin kara tabbatar da cewa ni dan Jam’iyyar APC ne kuma mai kishin siyasar kasar nan da ci gabanta. Kamar yadda kowa ya sani siyasa na da matsaloli sosai a kasar nan da ya zama dole a kawo sauyi mai ma’ana. Jam’iyar APC a jihar nan kowa na jin ita ce mai jiran gadon gwamnati mai karewa kuma za ta amshi gwamnati cikin lumana da yardar Allah. Jam’iyyar ta zo a lokacin da ya dace domin ceto kasar nan daga halin kunci da take ciki. A matsayina na dan siyasa ba ni da wani kulli da nake da shi ga kowa, duk mai son ya shiga cikin tafiyarmu ina yi masa murna, Allah Shi ke da mulki yana bayar da shi ga wanda Ya so a lokacin da Ya so.
Aminiya: A matsayinka na jigo a wannan jam’iyya yaya kake kallon rikicin da ke kokarin shake ta a wasu jihohi, kuma yaya dangantakarka da jagoran siyasarka Alhaji Attahiru Bafarawa?
Kebbe: To kamar yadda Hausawa ke cewa sai ‘banza ko mahaukaci ke raina mafari.’ Bafarawa ne ya karfafa ni ga shiga siyasa kuma ba zan taba musun haka ba, har abada muna nan cikin mutunci da girmama juna. Amma ka san siyasa kowa akwai abin da yake gani shi ne daidai da zai taimaki al’umma, to masu ra’ayi guda ne za su hadu tare su tafi tare koyaushe a bangarori daban-daban don cimma nasara. Maganar magoya bayana a bari mu gina jam’iyya tukun kafin sanin matakin dauka don lokacin zabe bai matso ba. Ni mai biyaya ne ga shugabannin jam’iyyata duk abin da suka ce ina kansa tare da goyon bayansa, na yarda da duk wani Gwamna da yake dan APC ne shi jagoran jam’iyyar a jiharsa, ba ni da wata jayayya. Matsayinsu shi ne nawa a koyaushe da masu jayayya da hukuncin shugabanni sun gane da sun bari a zo a yi tafiya tare a manta da duk wani bambanci domin ceto kasar nan daga halin da take ciki.
Aminiya: Jam’iyyar PDP a kasa ta zargi jam’iyyarku ta APC da cewa jam’iyyar Musulmi ce, me za ka ce?
Kebbe: Maganar cewa Jam’iiyar APC ta addinin ce ina ganin masu cewa hakan mutane ne da ba su san tarihin mutanen da ke cikin tafiyar ba, sa’annan sun jahilci siyasar addini. Idan ka dubi tarihin wannan jam’iYya Dokta Ogbunnaya Onu shugaban Jam’iyyar ANPP ne ya kirkiro da tunanin jam’iyyun adawa su hadu domin su fuskanci Jam’iyyar PDP mai mulki. Da aka yarda da tunaninsa aka kafa kwamiti karkashin Cif Tomi Ikimi wanda shi ne ya yi ungozoman ganin an haifi APC lafiya. Ban ga yadda wani zai gaya min cewa wadannan za su zauna a yi kafa jam’iyya ta Musulunci da su ba, wannan abin dariya ne kuma abin takaici ne, da ke nuna jam’iyya mai ci ta razana. Ina kiran da su fito su yi yekuwar abin da suka yi wa jama’a da abin da za su yi a shekaru masu zuwa, ba su yi kokarin wasa da tunanin talakawa ba, suna cusa musu kabilanci da bambancin addini. Idan ka dubi Bola Tinubu ya yi shekara takwas yana
Gwamnan Jihar Legas ba mu taba jin wani rikicin addini ya tashi ba duk da cibiyar kasuwanci ne ta kasar nan da ke da kabilu daban-daban. Ga shi kuma ya zama jagoran siyasa na yankinsu a can ne za ka ga mace da miji addininsu daban, yaya da kanensa addini daban. To yaya mutumen da ke jagorancin irin wannan yankin za a ce kuma yana jagorancin jam’iyyar wani addini? Gaskiya wannan ba magana ce mai kyau ba, yanayinmu a kasar nan bai yi kama da kasar Masar ba wanda shi ne PDP ta kamanta da shi, tana son ta yi wasa da tunanin talakawa.
Jami’an PDP su yi irin wannan kalami kan Janar Buhari inda suka rika danganta shi da mai tsananin kishin addini don a bata shi a wurin wadanda ba addininsu daya ba. Alhali sun san cewa Janar Buhari mutum ne mai kishin kasa amma ba su bari a gane hakan.
Aminiya: An dade ana yada cewa ka sayar da shari’arka ga Gwamna Wamakko kan kalubantar da ka yi masa a kotu game da zabensa ko gaskiya ne?
Kebbe: Na ji dadin wannan tambaya da ka yi min, cewa wai na sayar da shari’a wata magana ce da na taba jin ta kuma na ce ba zan yi magana a kanta ba. Domin ita karya ba a karyata ta, kyale ta ake yi ta karyata kanta da kanta. Lokacin da aka zo maganar shari’a na ce ba zan je kotu ba, da yawa cikinku sun sani amma lamarin siyasa ba na mutum daya ba ne, sai jam’iyyarmu ta yanke shawarar mu tafi kotu, sai kotun farko ta jefar da shari’armu na sake gaya musu ban goyi bayan a daukaka kara ba, amma aka daukaka daga nan ne na tabbatar wannan abin da ake yi ba zai haifa mana da mai ido ba, don ana bata mana lokaci ne kawai, na kira lauyana sauran wata daya lokacin da aka ba da na sauraren karar zabe ya kare, na tambaye shi wane irin sakamako ne kake zaton za mu samu a wannan shari’a? Sai ya gaya min har in har za mu samu nasara sai dai a ce mu koma kotu ta farko su saurari wannan shari’a mu nasara, nan ma sai sun ja a kotun sama duk kuma ana son a gama shi cikin wata daya. Na ce masa don Allah wace shawara zai ba ni, ya ce shari’ar nan a fita batunta kada a ci gaba da ita, na ce na amince ka janye karar a dainata, kuma wannan maganar da na fadi, Allah Ya san na fada wa Alhaji Attahiru Bafarawa ita, kuma wallahi maganar da ya gaya min ita ce: “Mutane sun ga kokarin da muka yi don haka bai da amfani mu ci gaba da aikin da ba ya da amfani,” haka muka yi da shi. An ce an hadu da ni a Dubai an ba ni miliyoyin Naira, tun kafin zaben 2012 da muka zauna a otel din Sakkwato Guest da shugaban hukumar zabe ta kasa kan yadda zabenmu zai kasance tare da ku ’yan jarida ban sake ganin Gwamna Wamakko ba, in ya ba da sako a ba ni ta hanyar wani ba a ba ni ba, ban amshi ko sisin kwabo daga Gwamna Wamakko don in janye shari’ar ba, wannan kage ne kawai. Maganar da muka taba yi ta waya, ita ce lokacin da na je wurin wata da ke da hulda da shi tana magana da shi ta ba mu muka gaisa har ya ba ni shawara kan shari’ar cewa shi yana kashe kudin yi wa jama’a aiki ni ko ina kashe kudina da mun bari da ya fi, haka aka yi muka janye shari’a, ban taba karbar kudin Gwamna Wamakko ba bai taba yi min hanya na samu wani abu ba, bai taba turo min da kudi ba.
Aminiya: Ko kana da wani sako ga al’ummar Jihar Sakkwato?
Kebbe: Sakona ga jama’ar Jihar Sakkwato muna son su ba wannan jam’iyya tamu APC goyon baya domin siyasa magana ce ta yawa, don haka mu fidda rayukanmu daga yin siyasa ta kudi. Sa’annan wani abu da nake ganin yana son kunno kai a cikinal’ummarmu shi ne kone-konen kayan jama’a, wannan ba dabi’a ce mai kyau ba, ya kamata iyaye da manya su ja hankulan ’ya’yansu kada wani ya tura su ga ayyukan ta’addanci.