Masu juna biyu sun mutu wajen rububin karbar abinci a Borno

Red Cross ta bayyana rashin jin dadinta kan faruwar lamarin.

Masu juna biyu sun mutu wajen rububin karbar abinci a Borno

Wasu mutane da sojoji suka ceto daga hannun mayakan Boko Haram/ISWAA a Jihar a Borno

Akalla mata 10 ne wadanda galibi masu juna biyu ne ko kuma masu shayarwa suka mutu yayin turmutsutsu wajen karbar abinci a garin Monguno da ke Jihar Borno.

Wannan hadari ya faru ne a lokacin da dubban ’yan gudun hijira da ke wani sansani suka fara rububin karbar abincin agaji da aka kai musu.

Kungiyar Red Cross ce ta rika raba abincin, wadda ta bayyana rashin jin dadinta kan faruwar lamarin.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa kungiyar ta Red Cross ta kuma kai kayan agaji domin taimakon wadanda suka yi rauni samakon hadarin.

Wata majiya ta jami’an tsaro ta ce mutane sun razana suna ta guje-guje bayan an harba hayaki mai sa hawaye a wurin domin tarwatsa taron.

A halin yanzu akwai sama da ’yan gudun hijira 100,00 da ke zaune a garin Monguno, wadanda galibi rikicin Boko Haram ne ya raba su da muhallansu.

Tsohon Kwamishinan Kano ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’