Masu juna biyu za su rika samun tallafin SURE-P a Jihar Bauchi
Mata masu juna biyu da suke zuwa awo da haihuwa a asibitocin Jihar Bauchi za su fara cin moriyar shirin Sure-P inda za a rika ba su Naira dubu 10 domin a tallafa musu musamman marasa karfi.Tuni Ma’aikatar Lafiya ta Jihar ta kaddamar da kwamitin aiwatar da shirin a karkashin jagorancin Kwamishinan Lafiya na Jihar […]
Mata masu juna biyu da suke zuwa awo da haihuwa a asibitocin Jihar Bauchi za su fara cin moriyar shirin Sure-P inda za a rika ba su Naira dubu 10 domin a tallafa musu musamman marasa karfi.
Tuni Ma’aikatar Lafiya ta Jihar ta kaddamar da kwamitin aiwatar da shirin a karkashin jagorancin Kwamishinan Lafiya na Jihar Dokta Sani Abubakar Malami, sai Shugaban Hukumar Lafiya a Daga Tushe na Jihar, Dokta Nisser Aliyu Umar, Sakatare, yayin da Sarkin Dass Alhaji Usman Bilyaminu da shugaban kungiyar CAN da Babban Limamin Bauchi Alhaji Bala Ahmed da wakiliya daga ma’aikatar mata da sauransu za su kasance wakilai.
Gwamnatin Tarayya ce a karkashin Hukumar Lafiya Daga Tushe ta fito da shiri a jihohin Zamfara da Bauchi da Kaduna da Neja da Anambra da Bayelsa da Ebonyi da Ogun, kamar yadda jami’in hukumar Dokta Isa Mohammed Jidda ya bayyana yayin kaddamar da kwamitin, wanda zai fara aikin gwaji a garuruwan Sade da Papa da Soro da Ganjuwa a Jihar Bauchi.
Dokta Isa Jidda ya ce shirin zai yi rajistar matan da suke zuwa awo tun farkon ciki har haihuwa inda za a ba kowace Naira dubu biyar lokacin da take da ciki, sannan bayan ta haihu a sake ba ta Naira 5000. Ya ce akwai bankunan musamman da za su shirya biyan matan a asibitoci a karkashin wani shirin CCT da asusun tallafin man fetir wato Sure-P, kuma an fara gwada shirin a asibitoci 36 na jihohin kasar nan.
A jawabin Mai martaba Sarkin Dass ya yi fatar za a cika manufofin shirin don ganin matan da aka yi dominsu ne kurum suka amfana, ba kudin su makale a hannun wasu mutane ba.
A jawabin Dokta Sani Malami ya yaba wa shirin wanda ya ce zai taimaki mata masu juna da kananan yara, saboda talauci da rashi ke sa mata ke mutuwa yayin goyon ciki ko lokacin haihuwa.
Shi ma Dokta Nisser Aliyu ya ce za a sa ido sosai wajen gani matan da aka fito da shirin dominsu ne kawai suka amfana.