Mali: Sojoji za su kafa gwamnatin riko ta farar hula

Sojojin da suka hambarar da gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita na Mali sun ce za su kafa gwamnatin riko ta farar hula da za ta gudanar da zabe da zai kawo sabuwar gwamnati a kasar. Sanarwar hakan na zuwa ne bayan Shugaban Keita ya sanar da saukarsa daga mukaminsa ‘domin guje wa ba zubar da […]

Mali: Sojoji za su kafa gwamnatin riko ta farar hula

Sojojin da suka hambarar da gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita na Mali sun ce za su kafa gwamnatin riko ta farar hula da za ta gudanar da zabe da zai kawo sabuwar gwamnati a kasar.

Sanarwar hakan na zuwa ne bayan Shugaban Keita ya sanar da saukarsa daga mukaminsa ‘domin guje wa ba zubar da jina a kasar’.

A wani jawabin da ya yi ta talbijin, kakakin sojoji da suka  yi juyin mulkin ya ce sun kifar da gwamnatin ne domin kawar da kasar daga kara fadawa cikin rikici.

A safiyar Laraba ce hambararren shugaban ya sanar da saukarsa daga mukaminsa a waji jawabi da ya yi ta talbijin, bayan shafi awanni a tsare.

Fusatattun sojoji da suka yi wa kansu lakabi da Kwamitin Kasa na Ceto Al’umma, sun tsare shi ne tare da firaminista Boubou Cisse, suka kuma tilasta musu sauka da mukamansu da rusa gwamnatinsu.

“Na yanke shawarar sauka daga mukamina”, kamar yadda hambararren Shugaba Keita ya ce a cikin jawabinsa.

An shafe watanni a Mali kasar na fama da rikicin siyasa bayan ‘yan adawa sun yi fatali da sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar a farkon wannan shekarar.

Masu zanga-zangar na kira da Shugaba Keita ya sauka daga mukaminsa saboda zargin rashawa da kuma gazawar gwamnaitnsa wajen yakar masu tayar da kayar baya.

Rikicin kasar ya yi kamarai ne a watan Yuli bayan an kashe wasu mutum 11 a cikin kwana uku da aka yi ana zanga-zangar.

‘Yan adawar kasar sun ki amincewa da tayin sulhu da gwamantin Mista Keita ta yi, suka kuma yi alkawarin ci gaba da gangamin adawa da gamnatinsa, duk da yunkurin kasashen duniya na sasanta tsakanin bangarorin.