Masu kai wa Boko Haram bayanai sun shiga hannu a Yobe

Majiyoyin tsaro sun ce dubun mutanen ta cika ne a ranar 4 ga Yuni, inda sojojin bataliya ta 120 Task Force Battalion da ke Goneri tare da haɗin gwiwar ’yan CJTF suka kama su.

Masu kai wa Boko Haram bayanai sun shiga hannu a Yobe

Rundunar Sojojin Operation Hadin Kai ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da kai wa ’yan ta’addar Boko Haram/ISWAP bayanai a a Jihar Yobe.

Majiyoyin tsaro sun ce dubun mutanen ta cika ne a ranar 4 ga Yuni, inda sojojin bataliya ta 120 Task Force Battalion da ke Goneri tare da haɗin gwiwar ’yan CJTF suka kama su.

Mutanen biyu, Gambo Bukar, mai shekara 28, daga ƙauyen Kimeri da Ahmad Ahmed, mai shekara 21, daga ƙauyen Yari, dukkansu ’yan Karamar Hukumar Gujba ne.

“Sojojin sun yi aiki bisa bayanan sirri masu inganci, kuma sun yi nasarar kama waɗanda ake zargin guda biyu. Ana ci gaba da ƙoƙarin kama wani mutum na uku da ake zargi wanda har yanzu ba a san inda yake ba,” in ji majiyar.

Daga baya an miƙa waɗanda ake zargin ga hukumomin soji domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su a gaban kotu.

Masu sharhi kan tsaro sun bayyana cewa irin waɗannan ayyukan leƙen asiri na da muhimmanci wajen dakile ta’addanci, domin suna taimakawa wajen wargaza hanyoyin tallafa wa ’yan ta’adda da kuma hana su samun bayanai da kayan aiki.