Masu kamuwa da cutar ƙyandar biri na ƙaruwa a Afirka — AU

An dai samu rahotannin bullar cutar a karon farko a Sweden da Pakistan.

Masu kamuwa da cutar ƙyandar biri na ƙaruwa a Afirka — AU

Hukumar Lafiya ta Tarayyar Afirka AU ta sanar da cewa adadin masu kamuwa da cutar ƙyandar biri na ƙaruwa a nahiyyar.

AU ta bayyana hakan ne yayin da ta fitar da alƙaluman mutum 18,737 da suka kamu da cutar ƙyandar biri tun daga farkon wannan shekara.

Hukumar ta ce a cikin wannan adadi, har da kimanin mutum 1,200 da suka harbu da cutar a mako guda.

Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Saurin Yaduwa ta Afirka ta ce an samu ɓullar cutar a ƙasashen nahiyyar 12.

Cibiyar ta ce kawo yanzu cutar  ta yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 541, da adadin mace-macen ya kai kashi 2.89 bisa 100.

Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana cutar ƙyandar biri wato mpox a matsayin gagarumar annoba da ke buƙatar ɗaukin gaggawa.

Cutar dai ta fi ƙamari a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kwango da annobar ta bazu a dukkan lardunan kasar 26.

Rahotanni daga Burundi na cewa an samu ɓullar cutar a mutane 173 da ake ci gaba da gudanar da bincike.

An dai samu rahotannin bullar cutar a karon farko a wajen nahiyar Afirka a ƙasashen Sweden da Pakistan.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano