Masu kananan sana’o’i sun koka da farautarsu da ake yi a Legas

Masu ‘yan kananan sana’o’i da kan dauki hajojin su a kai suna yawo a manyan titunan Legas da kan shatale-tale  na cigaba da kokawa duba da yadda jami’an gwamnati ke cigaba da farautar su, inda sukan kwace kayayyakin su kana  su tura su gidan jarun da tara mai yawa. Abubakar Hassan Muhammad, wanda ke sana’ar […]

Masu kananan sana’o’i sun koka da farautarsu da ake yi a Legas

Masu ‘yan kananan sana’o’i da kan dauki hajojin su a kai suna yawo a manyan titunan Legas da kan shatale-tale  na cigaba da kokawa duba da yadda jami’an gwamnati ke cigaba da farautar su, inda sukan kwace kayayyakin su kana  su tura su gidan jarun da tara mai yawa.

Abubakar Hassan Muhammad, wanda ke sana’ar sayar da kayayyakin mota, wadanda suka hadar da waifa da makamantansu ya shaida wa Aminiya cewa a halin da ake ciki a yanzu a Legas hankalin masu ƙananan sana’o’i  a tashe yake bisa la’akari da yadda jami’an gwamnatin ke kai musu farmaki a hanyar  neman abincin su, wacce ba ta saba wa dokar kasa ba.

“A yanzu Gwamnan Legas ya sanya doka duk wanda aka kama yana talla a ci tararsa Naira dubu 90 idan kuma ba ka da su a ɗaure  ka tsawon wata shida a gidan jarun. Don haka yanzu matasan mu cike suke a gidajen kaso na Jihar Legas, domin ba duk dan tallar da aka kama ke da dubu 90 ba. Ya kamata mahukuntan kasar nan su sani, ba mu da wata hanyar neman abincin da ta wuce wannan, da ita muke rike da kan mu, mu kuma kula da iyayen mu da ‘yan uwan mu. Wasunmu na da iyali da ita suke ci da su, su biya wa ‘ya’yansu makaranta. To idan an hana mu sana’ar sata ake so mu koma? “ inji shi.

Haka zalika Usman Abubakar matashi ne mai sana’ar tuƙin babur wato acaba ya koka da yadda a ‘yan kwanakin nan jami’an ‘yan sandan ke kwace musu babur, inda ya ce haka ake bin su loko da sako ana kwace musu babur  ana zubawa a babbar mota a tafi da su. Duk wanda aka karbi babur ɗinsa ya rasa shi ke nan.

 “Abin takaicin ma shi ne yadda ‘yan sandan ke zuwa cikin farin kaya suna karbe mana babur din mu, hakan ne yasa ‘yan batagari ke yin amfani da wannan dama suna tare mutanen mu su kwace musu baburan su, sai daga baya ka ga an koma gefen ana cin  kasuwar baburan da aka kame. Fatan mu a nan shi ne a saukaka mana idan Gwamnatin Legas ba ta san ganin ‘yan acaba ne sai ta sanar da mu mu hakura” inji shi.

A Talatar da ta gabata ne Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Legas Edigal Imohimi ya yi zama da manyan kungiyoyin masu tukin babur na Jihar Legas, inda a zaman nasu suka cinma daidaiton cewa daga ranar 2 ga watan Janairun shekara mai zuwa kowane mai tukin babur na haya dole ne ya yi rijista da kungiyar ‘yan achaɓa kana ya sanya rigar shaidar da aka tanadar musu, domin tsaftace harkar, tare da hana wa batagari shiga cikin su suna yi wa jama’a ta’annati, kana ya gargadi daukacin ‘yan acabar da su kasance masu bin dokokin tukin babur na jihar.