Masu kiran a binciki kisan Apo ba su nufin alheri ga kasar nan – Jonathan
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce shaidu sun nuna akwai ’yan Boko Haram a cikin wadanda aka kashe a wani gini da ba a kammala ba a Abuja a makon shekaranjiya, inda ya ce masu kiran a gudanar da bincike a kan kisan ba su nufin alheri ga kasar nan.Shugaba Jonathan ya bayyana haka […]
Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce shaidu sun nuna akwai ’yan Boko Haram a cikin wadanda aka kashe a wani gini da ba a kammala ba a Abuja a makon shekaranjiya, inda ya ce masu kiran a gudanar da bincike a kan kisan ba su nufin alheri ga kasar nan.
Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a tattaunawarsa da kafafen watsa labarai da aka nuna tare da watsawa kai-tsaye ga jama’ar kasar nan ta talabijin da rediyo.
Ya ce an yi masa bayani kan lamarin, kuma furucin wasu da aka kama bisa zargin ta’addanci ya nuna akwai ’yan Boko Haram a cikin wadanda aka kashen. Ya ce furucin wadanda ake zargin ya kuma nuna rashin alfanun kiraye-kirayen da wasu daidaikun mutane ke yi na a yi bincike kan lamarin.
“Wannan ya sa nake cewa a wasu lokuta, wasu daga cikin wadannan mutane da ke kiran a yi bincike ba su nufin alheri ga kasar nan,” inji shi.
Ya ce duk lokacin da aka fafata tsakanin jami’an tsaro da miyagu a wurin da jama’a ke zaune, akwai yiwuwar an hada da mutanen da ba su da laifi musamman idan aka yi amfani da bindiga.
Game da ko an kashe Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ko a’a, Shugaba Jonathan ya ce bai san ko ya mutu ko yana raye ba. “Ban sani ba, ko ya mutu ko yana raye. Ban san shi ba, kuma ban taba ganinsa ba a baya.”
Idan za a iya tunawa a ranar 19 ga Agusta ne Rundunar JTF ta fitar da sanarwar cewa akwai yiwuwar Shekau ya mutu sakamakon harbin bindiga da ya samu a lokacin fafatawa a dajin Sambisa a ranar 30 ga Yuni.
Sai dai a makon jiya wani faifan rediyo ya ruwaito Shekau yana cewa bai mutu ba, kuma ya dauki alhakin kashe-kashen fararen hula da aka yi a garin Benishek a Jihar Borno a ranar 17 ga Satumba.
Mahukuntan soja sun ce za su binciki faifan, sai dai kuma Shugaba Jonathan a matsayinsa na Babban Kwamandan Askarawan Najeriya da ke karbar bayanai daga dukkan shugabannin hukumomin tsaro a kullum ya ce bai da masaniya ko Shugaban Boko Haram din yana raye ko an kashe shi ba.
Wannan matsayi na Shugaban kasa ya zo ne a daidai lokacin da Majalisar Dattawa ta yanke shawarar bincikar kisan na Apo wanda ya ci rayukan mutum takwas tare da raunata 17 da aka tabbatar ’yan Keke-NAPEP ne da masu tura baro da suke zaune a wannan gini da ba a kammala ba