Masu kisa 13 da masu satar mutane 12 sun shiga hannu a Kaduna

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna ce ta sanar da haka tare da cewa wasu mutane, huɗu da ake zargi da satar motoci sun shiga hannunta a makonni biyu a fadin jihar

Masu kisa 13 da masu satar mutane 12 sun shiga hannu a Kaduna

’yan Sanda

Mutum 12 da ake zargi da aikata kisa da wasu 12 masu yin garkuwa da mutane sun shiga hannu a Jihar Kaduna a cikin mako biyu.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Kaduna ce ta sanar da haka tare da cewa wasu mutane, huɗu da ake zargi da satar motoci sun shiga hannunta a makonni biyu a fadin jihar.

Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Muhammad Rabiu, ya bayyana wa a taron manema labarai a ranar Litinin cewa rundunar ta kuma ƙwato motoci 4 da aka sace da kuma kwalaye 2,700 na maganin Tramadol da wasu miyagun ƙwayoyi.

Ya jaddada cewa rundunar ta himmatu wajen yaƙi da dukkan nau’o’in laifuka ta hanyar amfani da bayanan sirri, dabarun aiki na musamman da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da al’umma.

Rabiu ya ce waɗannan matakai sun haifar da nasarori, ciki har da kama manyan ’yan ta’adda, masu fyaɗe, da kuma ƙwace makamai da dukiyoyin da aka sace.

Ya ci gaba da cewa hakan ya nuna ƙudurin rundunar na hana ’yan ta’adda samun damar aikata laifi a Kaduna.

“Za mu ci gaba da ƙarfafa tattara bayanan sirri, inganta hulɗa da al’umma, da kuma gudanar da ayyuka na musamman kan ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane, ɓarayin mota da sauran laifuka,” in ji shi.

Kwamishinan ya gode wa Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Olatunji Rilwan Disu, bisa jagoranci da goyon baya, da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, bisa tallafi da haɗin kai da yake bai wa rundunar.

Ya kuma yaba wa jama’ar Kaduna bisa goyon baya da bayar da sahihan bayanai da suka taimaka wajen samun nasarori. Ya buƙaci al’umma su ci gaba da kasancewa cikin shiri da kuma yin aiki tare da ’yan sanda domin tabbatar da tsaro.

Rabiu ya kuma roki bangaren shari’a da ya ba ’yan sanda damar nuna waɗanda ake zargi, musamman waɗanda aka kama da laifi ko aka samu da hujjoji, domin ƙara wayar da kan jama’a da kuma taimakawa wajen hana aikata laifuka.