Masu kishin Arewa akwai kalubale a gabanmu
Arewa consultatibe Forum/kungiyar hankoron kare muradun Arewa. kunnenku nawa? A madadin ni kaina da duk wani iri na dan katsalandan da saka kai cikin abin da wasu za su kalla da fuska biyu ko shiga sharo ba shanu, ina kira da karamar muryar da nike fatan za ta girma zuwa gaba da cewa kifi na […]
Arewa consultatibe Forum/kungiyar hankoron kare muradun Arewa. kunnenku nawa? A madadin ni
kaina da duk wani iri na dan katsalandan da saka kai cikin abin da wasu za su kalla da fuska biyu ko
shiga sharo ba shanu, ina kira da karamar muryar da nike fatan za ta girma zuwa gaba da
cewa kifi na ganinku masu jajayen homa. Tambaya shin kun san Malam Abubakar Ladan Abubakar Zariya?
Masu kishin Arewa akwai kalubale a gabanmu. Lallai wajibi ne mu farka daga barcin da muke yi. Shata dai y ace ku tashi mu farka ‘’yan arewa mu san barci aikin kawai. Sai ya kare da cewa: “Idan ka farka b aka danno.”
idan kun sani ku kara sani in baku sani ba sai ku sani, shi ne wannan da ya fara fitowa da nahiyar Afrika sarari ta hanyar waka mai taken “….hada kanmu Afirika mu so juna” na tabbatar da kowa ya yarda da wannan gudummuwa ta Ala sai masu kallon waka ta fuskar da ta wuce guda daya tilo. Shin babu wani tanadi da ofishinku ya yi wa irin wadannan talikkai, gwiwarku ta yi kasa goshinku ya yi zufa kuna kasa warwas akan abin da Jaridar Aminiya ta buga na hirarta da dattijon mai shekaru sama da 80 yana barar gero da dawa da ‘yan kwabban kashewa, a bayyane ba boye ba.
A rashi ba chi da guni ko rashin godiyar Allah ba, ya kamata koda laifi wannan mai lambobin girmamawa ciki kuwa har da ta MON ya yi a yafe masa a tattala a tallafa a tarfa wa garinsa nono. Ni dai idan da a ce akwai hanyar da zan tofa yawu na gare shi fiye da haka su yi tasiri da na yi kundumbala da kunar bakin waken iyakar nawa
Gudun ruwa koda kuwa ina komawa amsar sufari ga makotana ko neman algararar tanadin tumu da ya bari kan iyakar gonaki. ina fatan masu hannu da shuni da wadanda abin ya shafa za su tuna da cewa ba su zo da komai duniya ba, kuma haka za su barta hannu rabbana, ba a shuka kabewa a girbi kabushi.
Wassalam, Marubucin ya fito daga Tambuwal ta Jihar Sakkwato a Najeriya, adosedtf@ gmail.com.