Masu koyon tukin mota sun zarce cikin wurin ninkaya

Wata motar da ake amfani da ita don koya wa wata mace tuki ta zarce cikin wurin nikaya bayan motar ta tsallake wani shinge ta fada cikin ruwa. Kakakin Hukumar Kashe Gobara da Bayar da Agaji ta yankin Montgomery da ke Maryland a Amurka, Pete Piringer ya bayyana wa jaridar Washington Post cewa, mutanen da […]

Masu koyon tukin mota sun zarce cikin wurin ninkaya
Masu koyon tukin mota sun zarce cikin wurin ninkaya

Wata motar da ake amfani da ita don koya wa wata mace tuki ta zarce cikin wurin nikaya bayan motar ta tsallake wani shinge ta fada cikin ruwa.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara da Bayar da Agaji ta yankin Montgomery da ke Maryland a Amurka, Pete Piringer ya bayyana wa jaridar Washington Post cewa, mutanen da suke cikin motar ba su samu rauni ba duk da fadawar motar cikin ruwa, saboda abu ne da bai cika faruwa ba mota ta yi nutso a ruwa.

Piringer ya ce, hadarin ya faru ne lokacin da wani mai koyar da tukin mota yake tare da wata da yake koya wa tuki inda kafin su ankara sai cikin ruwan nikaya na North Creek da ke Center Pool.

Piringer ya ce, wani mutum da wata mata na tsaye a kusa da wurin nikaya lokacin da jami’an bayar da agajin suka hallara a wajen don ceto motar da ta fada cikin ruwan. 

Sai dai babu cikakken bayani a kan hadarin.

Dalilin da ba zan bai wa Gwamnatin Tinubu shawara ba — Sarki Sanusi

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana