Masu kuɗi ya kamata a ƙara wa haraji —Farfesa Ɗandago

Farfesa Kabiru Isa Ɗandago ya ce maimakon a ƙara wa talakawa haraji, kamata ya yi a soke karɓar Harajin VAT, a ɓullo da haraji a kan sayayyar da masu kuɗi suka yi da na sayen kayan alfarma da na mallakar kadarori

Masu kuɗi ya kamata a ƙara wa haraji —Farfesa Ɗandago

Masanin tattalin arziƙi kuma ƙwararre a fannin haraji, Farfesa Kabiru Isa Ɗandago, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara harajin da take karɓa daga mawadata, maimakon ƙarin harajin sayen kayayyaki (VAT).

Farfesa Ɗandago, ya ce ya kamata gwmanati ta soke Harajin VAT, ta ɓullo da harajin mallakar kadarori da harajin sayen kayan alfarma.

A cewarsa, yin hakan zai da gwmanatin ta samu ninkin kuɗaɗen shiga da take samu daga VAT a halin yanzu.

Farfesan fannin aikin Akantan, ya bayyana cewa karɓar waɗannan harajin zai rage bambancin talaka mai kudi, saboda masu kuɗi ne za su fi biyan haraji.

“Misali a sanya haraji a kan abubuwan alfarma da waɗanda mawadata suka saya,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa waɗannan nau’ikan haraji “za su sama wa gwamnati ninki biyu na abin da take samu daga VAT.”

Ya sanar da haka ne a yayin hirar da kafar Trust TV ta yi da shi kan ƙudirin sabuwar dokar haraji da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aike wa majalisar, wanda ke ci gaba da haifar da ce-ce-ku-ce.

Farfesa Ɗandago ya kuma bayyana damuwa game da harajin dukiyar iyalai da ke cikin sabuwar dokar, yana mai fargabar cewa hakan na iya nufin karɓar haraji a kan dukiyar gado ko waɗanda na kyauta.

Ba da talakawa gwamnonin Arewa suke yi ba —Yusuf

A nasa ɓangaren, masanin tattalin arziƙi kuma ƙwararre a fannin siyasa, Baba Yusuf, ya bayyana cewa ba don kishin talakawan gwamnonin Arewa suke adawa da ƙudurorin dokar harajin ba.

Ya bayyana dalilin shi ne yadda gwamnonin suka yi shiru a lokacin da aka cire tallafin mai, saboda hakan ya kara musu kuɗaɗen da suke samu daga asusun tarayya.

Amma da yake dokar harajin za ta rage abin da suke samu sai suka fito suna Aswad da ita — don kansu suke yi ba don kishi ko tausayin talakawa ba.

A jira tukuna —Ɗan kasuwa

Shi kuma ɗan kasuwa Nuruddeen GwamnaYero, ya bukaci a dakatar da batun sabuwar dokar harajin da ke ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce.

HammanYero ya bayyana cewa shura tukuna sai an ga alfanon matakan tattalin arzikin da gwmanatin ta ɗauka — na cire tallafin mai da tsarin canjin kuɗaɗe — a zahiri tukuna.