Masu kudin da suka yi alkawarin bayar da rabin dukiyoyinsu don taimakon jama’a
Wasu mutane da suka mallaki biliyoyin Daloli sun yi alkawarin bayar da kyautar rabin dukiyoyinsu domin tallafawa mutanen duniya. Wannan shirin na bayar da kyautar rabin dukiyar dai Bill Gates da Warren Buffett ne suka assasa, sannan kuma ya zuwa yanzu wasu mutane su 14 sun amince su shiga cikin tsarin, inda suka ce za […]

Wasu mutane da suka mallaki biliyoyin Daloli sun yi alkawarin bayar da kyautar rabin dukiyoyinsu domin tallafawa mutanen duniya.
Wannan shirin na bayar da kyautar rabin dukiyar dai Bill Gates da Warren Buffett ne suka assasa, sannan kuma ya zuwa yanzu wasu mutane su 14 sun amince su shiga cikin tsarin, inda suka ce za su yi amfani da dukiyoyinsu ne wajen magance talauci, gyara muhalli da canjin yanayi.
Wadannan mutane su 14 ‘yan kasuwa ne da suke yi fice a harkokin kasuwanci a kasashensu. Rabin dukiyoyin wadannan mutane su 16 zai kai kimanin Dala biliyan 99.
Daga cikinsu akwai dan kasar Tanzania Mohammed Dewji mai kimanin shekara 42. Shi ne karaminsu, kuma wanda ya fi kowa tarin dukiya a kasar Tanzania inda yake da kimanin Dala biliyan 1.39.
A cewar shi “Ya kamata muma mu taimakawa mutane ta yadda ya kamata,” inji shugaban Kamfanin MeTl, Mohammed Dewji na kasar Tanzania.
Wadanda suka shiga cikin tsarin su ne:
1. Bill Gates
Yana da kimanin dala biliyan $90.3. Bill Gate da matarsa Melinda sune suke da gidaunaiyar Bill $ Melinda wadda ita ce gidauniya ma fi taimakon al’umma a duniya. Bill gate ya kasance wanda ya fi kowa tarin dukiya a duniya sau 18 a cikin 23 da jaridar Forbes ke wallafawa a duk shekara, ciki har da wannan shekarar. Daga cikin ayyukan taimakon da ya yi akwai, harkokin taimakon harkar lafiya da fafutukar kare yaduwar cutar Poliyo a duniya. A karshen shekarar 2016 ne Bill Gate ya gabatar da tallafain dala biliyan 1 tare da wasu mutane 20.
2. Warren Buffett
dan kasar Amurka ne mai shekara 86, kuma shi ne shugaban kamfanin Berkshire Hathaway yana da kimanin dala biliyan $74.4. Warren wanda ake wa lakabi da Oracle of Omaha, yana daya daga cikin manyan kasuwan duniya. Kamfaninshi na Berkshire Hathaway na kamfanoni sama da 60 a karkashinshi, wadanda suka hada da Geico, Duracell da Dairy kueen. Ya zuwa yanzu ya bayar da kimamin dala biliyan $32 kyauta, kuma ya yi alkawarin bayar da kasha 99 na dukiyarsa domin taimakon al’umma.
3. Leonard H. Ainsworth
Leonard H. Ainsworth dan asalin kasar Asutrelia ne, kuma yana da kimanin shekara 92 a rayuwa. A yanzu haka dai shi ne shugaban Kamfanin Ainsworth Game Technology Ltd, kuma ya yi taba yin aiki a matsayin Manajin Darakta na Kamfanin Aristocrat Leisure Ltd. Sannan kuma ana tunanin dukiyarshi za ta kai kimanin dala biliyan $1.1.
4. Mohammed Dewji
Mohammed Dewji wani dan kasuwa ne dan asalin kasar Tanzani mai shekara 42 wanda ya dade yana taimakon jama’a a kasar Tanzania a matsayinshi na wanda ya fi kowa arziki a kasar, kuma tsohon dan siyasa ne. Shi ne shugaban Kamfanin MeTl Group, kuma dukiyarshi ta kai kimanin Dala biliyan 1.39.
5. Dagmar Dolby
Dagmar ’yar kasar Amurka, amma haifaffiyar kasar Jamus. Tana da shekara 76, kuma tana da kimanin dala biliyan $3.5 kamar yadda Forbes ta sanar.
6. Kjell Inge Røkke
Kjell Inge Røkke dan kasuwa ne dan kasar Norway, kuma yana cikin wadanda suka fi kudi a kasar. Shi ne shugaban Kamfanin Aker ASA. Kuma yana kimanin dala biliyan $2.6. Kuma a yanzu yana da shekara 58.
7. Stelios Haji-Ioannou
Stelios Haji-Ioannou dan asalin Girka ne amma mazaunin Monaco na kasar Faransa. dan shekara 50 ne a rayuwa kuma shi ne shugaban kamfanin easyJet, kuma ya samu jari ne daga mahaifinshi. Kuma yana da kimanin dala biliyan 1.3.
Sauran su ne:
8. Nick da Leslie Hanauer: Shugabannin kamfanin benture capitalist and founder of Cibic bentures, kuma suna da kumanin dala biliyan $1.
9. Iza da Samo Login: ’Yan kasar Slobenia, kuma su ne shugabannin kamfanin nishadi na Outfit7. Kuma suna da kimanin dala dala biliyan $1.
10. Dean da Marianne Metropoulos: ’Yan kasar Amurka ne, kuma su ne shugabannin Kamfanin Pribate ekuity firm Metropoulos & Co. kuma suna da kimanin dala biliyan $2.4.
11. Terry da Susan Ragon: ’Yan kasar Amurka ne, kuma su ne shugabannin Kamfanin InterSystems Corp. kuma suna da kimanin dala biliyan $2.
12. Nat Simons da Laura Badter-Simons: ’Yan kasar Amurka ne, kuma shugabannin kasuwancin Inbestment management firm Meritage Group; wadanda suka assasa Sea Change Foundation. Suna da kimanin dala biliyan $12.
13. Robert Frederick Smith: dan asalin kasar Amurka ne, kuma shi ne ya shugaban kamfanin bista Ekuity partners. Kuma yana da kimanin dala biliyan 2.5.
14. Harry H. Stine: dan asalin kasar Amurka ne, kuma shi ne shugaban Kamfanin Stine Seed. Kuma yana da kimanin dala biliyan 3.3.
15. YOU Zhonghui: ’Yar kasar Chana ce, kuma ita ce shugaban Kamfanin Shenzhen Seaskyland Inbestment Holdings Group.
16. DONG Fangjun: dan kasar Chana kuma shugaban Kamfanin Dongfang Huikuan Financial Holdings.