Masu kwacen waya sun caka wa budurwa wuka a Yobe

Bata-gari da ke kwacen waya sun caka wa wata budurwa wuka a gadon baya a garin Damaturu, fadar Jihar Yobe.

Masu kwacen waya sun caka wa budurwa wuka a Yobe

wuka

Bata-gari da ke kwacen wayar sun caka wa wata budurwa wuka a gadon baya, suka karbe wayarta, sannan suka tsere a Damaturu, fadar Jihar Yobe.

Aminiya ta gano cewa da misalin karfe 9.15 na daren Asabar ne gungun matasan suka far wa wasu mata da ke kan hanyar zuwa unguwar Malari suka kwace musu wayoyinsu da ’yan kudadensu sannan suka caka wa daya daga cikinsu waka kafin su tsere su bar ta jina-jina.

Daga nan aka garzaya da budurwar mai shekaru 24 zuwa babban asibitin jihar da ke garin na Damaturu don domin ba ta daukin gaggawa.

Wannan irin aika-aika da matasan suka bullo da shi dai na barazana, musamman ga mata, manya da kanana, domin su ne matasan suka fi kai wa farmaki.

Ko a kwanan baya ’yan sanda da hadin gwiwar jami’an Sibil Difens (NSCDC) da ’yan sa-kai sun yin sintiri a wuraren da bata-gari ke taruwa don shaye-shaye suna Cafke su, mata da mazansu.

Al’ummar garin na Damaturu na cikin fargaba sakamakon ayyukan bata-garin, da ke hana su sakat.

Jama’ar garin na ganin muddin hukumoin tsaro ba su dauki matakin ba sani ba sabo ba kan masau wannan aika-aika, to kuwa tsugune ba za ta kare ba.

Wasu kuma na ganin akwai bukatar da gwamnatin jihar ta kara kaimi wajen samar wa matasa aikin yi da ba su horo kan sana’o’in da a karshe za a samar musu jari don dogaro da kansu; idan ba haka aka yi ba, to kuwa da sauran rina a kaba.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja