Masu laifi 93 sun shiga hannun ’yan sanda a Kano

Ana zargin wadanda da aka kama da shirin kawo cikas ga rantsar da sabon gwamnan Jihar.

Masu laifi 93 sun shiga hannun ’yan sanda a Kano

‘Yan sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta kama mutum 93 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban cikin mako guda a jihar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Muhammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba.

Gumel ya bayyana cewa binciken farko da suka gudanar ya tabbatar da cewa wadanda ake zargin na da hannu wajen daukar nauyin kawo cikas a bikin rantsar da sabon gwamna da mataimakinsa a Jihar.

Ya ce an samu wasu daga cikinsu dauke da muggan makamai, “da miyagun kwayoyi da kuma shirye-shiryen amfani da makaman domin yin fashi da kuma kawo cikas ga bikin rantsar da sabon gwamna.

“Don haka duk wadanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu kan wadannan laifuka.

“Ina da yakinin cewa kotunan shari’a za su dauki matakan da suka dace.”