Masu maganin gargajiya sun bukaci a binciki kashe wakilansu biyar a Jihar Neja

kungiyar masu Maganin Gargajiya ta kasa ta bukaci Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya da Daraktan Hukumar Tsaron kasa (SSS) su sanya a yi bincike kan kisan gillar aka yi wakilan kungiyar biyar a garin Tegina da ke Jihar Neja.Wata takardar kuka dauke da sanya hannun Sakataren kungiyar ta kasa Dokta Adamu Umar Baffa ta […]

Masu maganin gargajiya sun bukaci a binciki kashe wakilansu biyar a Jihar Neja
Masu maganin gargajiya sun bukaci a binciki kashe wakilansu biyar a Jihar Neja

kungiyar masu Maganin Gargajiya ta kasa ta bukaci Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya da Daraktan Hukumar Tsaron kasa (SSS) su sanya a yi bincike kan kisan gillar aka yi wakilan kungiyar biyar a garin Tegina da ke Jihar Neja.
Wata takardar kuka dauke da sanya hannun Sakataren kungiyar ta kasa Dokta Adamu Umar Baffa ta ce, an yi kisan gilla ta hanyar yankan rago ga ’ya’yan kungiyar da suka hada da Dokta Usman Sule da Bashir Sule da Aminu Musa da Abu da Yasa’a Isa dukkansu mutanen Dustinma da ke Jihar Katsina kuma suke zaune a Tegina fiye da shekara guda ta gabata.
Takardar ta ce, “A ranar 27 ga Yunin bana bayan sun dawo daga sayar da magani sun ajiye motarsu sun kwanta barci cikin dare wasu mutane sun shiga garin Tegina suka tashe su suka daure su da igiya washegari 28 ga Yuni suka yi musu duka sannan suka yi musu yankan rago.”
kungiyar ta ce wannan babban kalubale ne ga masu magungunan gargajiya a Najeriya, inda ta ce bayan su an kwantar da wasu wakilanta shida za a yanka Allah Ya kawo wasu mutane suka kwace su.
kungiyar ta ce, duk wadannan abubuwa an yi su ne alhali akwai hakimi da babban jami’an ’yan sanda da jami’an tsaro suna garin, inda ta ce bat a sani ba ko a Jihar Neja, musamman a Tegina wasu jama’a ne ke tafiyar da tsaro ta yadda za su rika daukar doka a hannunsu.
kungiyar ta koka kan yadda babban jami’in ’yan sandan Tegina da na Kagara da hedkwatar ’yan sandan Neja ke rikon sakainar kashi kan lamarin, inda ta ce har yanzu ba a nuna musu gawarwakin wakilan nasu da aka kashe ba, haka dukiyarsu, balle a gano wadanda suka yi aika-aikar.