Masu mu’amala da fasahar intanet a duniya sun kusa biliyan uku
Kamar yadda ta saba, Hukumar Lura da Harkar Sadarwa ta Duniya (International Tele-communication Union-ITU) ta fitar da alkaluman adadin masu shawagi a giza-gizan sadarwa ta duniya ta amfani da dukkan kayayyakin sadarwa a duniyar yau. Wannan rahoto nata, wanda shi ne kashi na farko a zangon rabin shekara, ya tabbatar da cewa a yanzu kashi […]
Kamar yadda ta saba, Hukumar Lura da Harkar Sadarwa ta Duniya (International Tele-communication Union-ITU) ta fitar da alkaluman adadin masu shawagi a giza-gizan sadarwa ta duniya ta amfani da dukkan kayayyakin sadarwa a duniyar yau. Wannan rahoto nata, wanda shi ne kashi na farko a zangon rabin shekara, ya tabbatar da cewa a yanzu kashi 40 ne cikin 100, wato mutum biliyan biyu da miliyan dari bakwai (2.7billion) a duniya ne suke mu’amala da fasahar Intanet.
A wannan rahoto da ta fitar cikin watan da ya gabata, hukumar ta sanar da cewa ya zuwa tsakiyar wannan shekara ta 2013, masu mu’amala da fasahar Intanet a duniya sun doshi biliyan 3! Wannan adadi kuwa shi ne kashi 40 cikin 100 na jama’ar duniya baki daya. Cikin wannan kaso, kasashe masu tasowa na da kashi 31, a yayin da sauran kashi 79 daga kasashe masu arziki ne. Wannan, a cewar hukumar, ya dada fito da katafariyar tazarar da ke tsakanin kasashe masu arziki da marasa galihu ne, musamman a fagen sadarwa ta duniya. Amma akwai alamar cewa kasashe masu tasowa lallai sun fara tasowa, musamman ganin yadda suke ta hankoron tabbatar da tsarin sadarwar bayanai ta Intanet mafi inganci, wato Broadband, da inganta tsarin sadarwar wayar salula da sauran hanyoyi.
A daya bangaren kuma, hukumar ITU ta tabbatar da cewa kasashen Turai (Europe) ne suke da kaso mai girma na adadin jama’a a giza-gizan sadarwa ta Intanet. Domin cikin duk mutum 4, to, 3 na da hanyar sadarwa ta Intanet. Sai kasar Amurka da ta biyo baya da kashi 61, da nahiyar Afirka mai kashi 16, sai kuma nahiyar Asiya mai dauke da kashi 50 cikin 100. A nahiyar Asiya kowane mutum daya cikin mutane uku, ya mallaki hanyar sadarwa ta Intanet.
A bangaren jinsi kuma, hukumar ta nuna cewa an samu karin adadi da kaso a bangaren mata masu mu’amala da wannan fasaha a duniya, inda kasonsu (percentage) ya karu da kashi 16. A yanzu akwai maza sama da biliyan daya da miliyan dari biyar masu mu’amala da fasahar Intanet a duniya da mata sama da biliyan daya da miliyan dari uku. Wannan ya cilla kason maza zuwa kashi 41 cikin 100, su kuma mata kasonsu ya haura zuwa kashi 37 cikin 100 a duniya. A kasashe masu tasowa mata masu mu’amala da fasahar Intanet sun kai miliyan 826, a yayin da maza suka haura zuwa miliyan 980. A kasashe masu arziki kuma wannan adadi ya sha bamban, a yayin da adadin maza masu mu’amala da fasahar ya tsaya a miliyan 475, adadin mata ya haura zuwa miliyan 483.
Dangane da ci gaban sadarwa a gidajen jama’a kuwa, hukumar ta nuna cewa daga cikin gidaje miliyan 750, kashi 41 a jone suke da fasahar Intanet. Daga cikin wannan adadi, kaso 28 daga cikin wadannan gidaje na kasashe ne masu tasowa, a yayin da kashi 78 daga kasashe ne masu arziki. Hukumar ta ci gaba da cewa bayan wadannan gidaje masu jone da fasahar Intanet, a duniyar yau akwai gidaje sama da biliyan daya da miliyan dari daya da har yanzu ba su samu alfarmar jonuwa da fasahar Intanet ba. Daga cikin wannan adadi, inji wannan rahoto, kashi 90 na gidajen na kasashe ne masu tasowa, a yayin da sauran ke kasashe masu arziki. Nahiyar Turai ce ke da gidaje masu jone da fasahar Intanet sama da kowace nahiya ta duniya. Domin, a cewarta, kashi 77 na gidajen da ke Turai duk a jone suke. A yayin nahiyarmu ta gado, Afirka, ke dauke da kashi 7 kacal cikin gidajen da ke jone da fasahar Intanet. A nahiyar Afirka kuwa, bincike ya nuna cewa tsakanin shekarar 2009 zuwa 2013, gidaje masu jone da fasahar Intanet sun karu da kashi 27; a nahiyar Asiya kuma da kashi 15, haka ma a kasashen Larabawa.
A bangaren kudancin Amurka kuwa, wato Latin America, kashi 61 suna mu’amala da fasahar Intanet. Idan muka koma kasashen Larabawa kuma, rahoton ya nuna cewa a cikin duk mutum uku, daya na mu’amala da fasahar Intanet. Kamfanin binciken ci gaban kimiyyar sadarwar zamani mai suna McKinsey & Co, ya yi hasashen karuwar masu mu’amala da fasahar Intanet a Indiya daga miliyan 160 zuwa miliyan 330 ya zuwa shekara ta 2015. A nata bangaren kuma hukumar ITU ta yi hasashen karuwar masu amfani da tsarin Broadband, duk dai a kasar ta Indiya, daga miliyan 175 zuwa miliyan 600 nan da shekara ta 2020.
Masana a tsarin sadarwar zamani sun nuna cewa daga cikin manyan dalilan da ke haddasa habakar masu mu’amala da fasahar Intanet a kasashe masu tasowa musamman, akwai yaduwar wayoyin salula masu dauke da tsarin sadarwa ta GSM. Sukan buga misali da Najeriya, inda a shekarar 2000, daidai sadda aka baiwa kamfanonin wayar salula lasisi, masu amfani da wayoyin salula ba su shige dubu dari biyar ba. Amma ya zuwa wannan shekara akwai masu amfani da layin wayar salula da kamfanonin wayar kasar suka bayar, kusan miliyan 100! A daya bangaren kuma, akwai karancin yaduwar fasahar Intanet a gidajen mutane a nahiyar Afirka musamman, ba don komai ba sai don dalilin farko. Galibin jama’a sun gwammace su yi mu’amala da fasahar Intanet ta hanyar wayar salula ko na’urorin mu’amala da bayanai na zamani, irin su iPad, da Samsung Galady Note, a misali. Maimakon sayen kwamfutoci, mutane sun gwammace, kuma ya fi musu sauki, su gudanar da ayyukansu ta amfani da wadannan na’urori.
Wasu Daga Cikin Tambayoyinku
Assalaamu Alaikum Baban Sadik, Allah kara hikima da basira, amin. Don Allah ina son ka turo mini kasidar nan wacce ka yi kan haske, wato: Light. Ga adireshin Imel dina: [email protected]. Ka kasance cikin koshin lafiya, sako daga: Yahuza Idris Hotoron Arewa, Tunshama, ketare, Kano: 08095588320
Wa alaikumus salam, Malam Yahuza ina godiya matuka. Na kuma cillo maka kasidar, amma makalawa na yi a jikin sakon, don haka sai ka saukar (Download) kafin ka iya budewa. Har wa yau, idan wayarka ba ta iya bude bayanai da aka taskance da masarrafar Microsoft Word, to dole sai ka je mashakatar lilo (Cyber Cafe) ka ciro. Allah sa a dace, amin.
Salaamun Alaikum Baban Sadik, da fatan alheri gare ka. Shin, wadanne abubuwa ne ake ce musu “The Seben Wonders of the World?” Sannan kwanakin baya ka yi bayani kan fasahar Bluetooth, ka ce akwai tabarau mai dauke da wannan fasaha. Don Allah ina son karin bayani. Daga Ummu Haidar, Gombe.
Wa alaikumus salam, dubun gaisuwa da fatan alheri ga Maman Haidar, Allah saka da alheri, amin. Wadannan abubuwa da ake kira “The Seben Wonders of the World” wato abubuwa bakwai masu ban mamaki a duniya, wasu al’amura ne ko wurare, ko wasu nau’ukan fasaha/ilimi da aka gano tasirinsu a duniya a wani lokaci na musamman. Shi ya sa tantance su ma yake da wahala. Domin abubuwa ne ko wurare ne da suka shafi zamunna daban-daban, da kasashe daban-daban. Don haka, cewa ga wadannan abubuwa da a duniya su kadai ake kira da wannan lakabi, ba abu ba ne mai yiwuwa. Akwai abubuwa guda bakwai masu ban mamaki da suka shafi ilimin sararin samaniya kadai, wato: Seben Wonders of the Solar System. Akwai wadanda suka shafi karkashin teku; akwai wadanda suka shafi fannin kere-kere; akwai wadanda suka shafi wasu kasashe kadai; akwai wadanda kuma wasu mujallun kasar Amurka da suka tantance a matsayin su ne abubuwa bakwai masu ban mamaki a duniya. Don haka, idan aka ce za a yi magana kan abubuwa bakwai masu ban mamaki a duniya, to dole ne a tsawaita bayani, don tantance su, da tsari ko yanayin da aka yi la’akari da shi/su, da dai sauransu. Tambaya irin wannan, mai harshen damo kuwa, ba abu ba ne da zai iya samar da amsa ta kai tsaye.
bangaren tambayarki na biyu kuma kamar yadda kika ce, na yi bayani kan samuwar nau’in fasahar Bluetooth da ke lake a jikin tabarau. Wannan tabbas yana nan, kuma amfaninsa shi ne aiwatar da tsarin sadarwa tsakanin wayar salularka ko kwamfutar da kake amfani da ita mai dauke da wakokin da kake son sauraro ta amfani da lasifikar wannan tabarau, don sauraro kai-tsaye ba tare da wata matsala ba. Ba wannan kadai ba, akwai na’urar sauraren wake na jikin mota mai dauke da fasahar Bluetooth; akwai talabijin mai dauke da fasahar Bluetooth, da dai sauran kayayyaki/na’urori/fasahar sadarwa na zamani. Da fatan kin gamsu.