Masu mu’amala da miyagun kwayoyi na karuwa a sansanonin ’yan gudun hijira

Wani bincike da Asibitin Kula da Lafiyar kwakwalwa ta Tarayya da ke Maiduguri ya yi ya gano cewa ana samun karuwar matasa masu tu’ammali da miyagun kwayoyi a sansanonin ‘’yan gudun hijirar Boko Haram 22 da ke garin Maiduguri. Binciken ya gano cewa an samu matasa sama da 4,700 a bara da ke tu’ammali da […]

Masu mu’amala da miyagun kwayoyi na karuwa a sansanonin ’yan gudun hijira
Masu mu’amala da miyagun kwayoyi na karuwa a sansanonin ’yan gudun hijira

Wani bincike da Asibitin Kula da Lafiyar kwakwalwa ta Tarayya da ke Maiduguri ya yi ya gano cewa ana samun karuwar matasa masu tu’ammali da miyagun kwayoyi a sansanonin ‘’yan gudun hijirar Boko Haram 22 da ke garin Maiduguri.

Binciken ya gano cewa an samu matasa sama da 4,700 a bara da ke tu’ammali da miyagun kwayoyin.
Wani babban jami’i a Asibitin Masu Tabin Hankali na Tarayya da ke Maiduguri Malam Babagana Machina, ya shaida wa wakilnmu cewa sakamakon matsalar rashin tsaro da ta addabi Jihar Borno da yakin Boko Haram ya daidaita, mutanen da suka yi gudun hijirar dole, inda suka rabu da sana’o’insu, ya haifar da karuwar matasa masu shekara 20 zuwa 30 da suke tu’ammali da miyagun kwayoyi da kashi 70 cikin 100.
Ya ce a shekara guda kawai asibitin ya samu sama da matasa 4,700, a tsakanin ‘’yan gudun hijirar, yayin da kuma alkaluma suka nuna cewa cikin shekara biyar sun samu matasa masu tabin hankali saboda shan miyagun kwayoyi sama da dubu 40, a jihar.
Ya ce sun hada hannu da gwamnatin jihar don aikin wayar da kan matasa, musamman a sansanonin ’yan gudun hijirar, inda ya roki iyayen yara musamman masu gudun hijira su sanya ido kan tarbiyyar ’ya’yansu don a dakile wannan mummunar dabi’a.
Shugaban Kwamitin Gwamnatin Jihar Borno don yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi a sansanonin ’yan gudun hijirar, Antoni Janar na Jihar Mai shari’a Kaka Shehu Lawan, ya ce sun hada gwiwa da Hukumar Yaki da Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) da Asibitin Kula da Tababbu don dakile yaduwar tu’ammali da miyagun kwayoyi a sansanonin.
A makon jiya ne aka gudanar da bikin yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi wanda Majalisar dinkin Duniya ta ware ranar 27 ga watan Yuni kowace shekara don gudanar da wannan biki. A Jihar Borno Hukumar NDLEA ta shirya bikin inda aka samu halartar kungiyoyin matasa da dama.