Masu mutunci da kishin kasa kwai zan nada ministoci – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nanata cewa masu kishin kasa da mutunci kuma kwararrun ’yan Najeriya ne kawai zai nada a matsayin ministoci a gwamnatinsa. Shugaba Buhari wanda ya bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata yana amsa tambayoyi a wani shirin talabijin mai suna Good Morning Nigeria, inda ya ce ’yan siyasa da […]
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nanata cewa masu kishin kasa da mutunci kuma kwararrun ’yan Najeriya ne kawai zai nada a matsayin ministoci a gwamnatinsa.
Shugaba Buhari wanda ya bayyana haka a ranar Litinin da ta gabata yana amsa tambayoyi a wani shirin talabijin mai suna Good Morning Nigeria, inda ya ce ’yan siyasa da kwararru za su samu ministocin.
“Daga abin da na gani a yanzu, muna bukatar ’yan Najeriya masu kishin kasa – ’yan Najeriya da za su yi aiki wurjanjan, masu ilimi da gogewa da sadaukar da kai – da ba su ci amana ba. Kowa ya yi don kansa da kuma Ubangijinsa don amfaninmu; abin takaici muna da mutane masu ilimi da kwarewa amma kowa kansa kawai ya sani – nawa zai samu cikin kankanen lokaci.”
Shugaba Buhari ya kara da cewa: “Kuma za mu duba ’yan siyasa da kwararru, amma hakika za mu zakulo masu mutunci a wadannan ajujuwa mu dora musu nauyin kula da ma’aikatu da muhimman hukumomin gwamnati.”
Dangane da rahoton sama-da-fadi a bangaren man fetur da gas, Shugaban kasar ya ce, Gwamnatin Tarayya tana aiki sosai wajen bankadowa da fallasa mutanen da suke wannan haramtaccen aiki.
Ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sanar da jama’a kan binciken da take yi kan lamarin.
Buhari ya ce manufar gwamnati ta gano tare da hukunta dukkan wadanda suke da hannu a aika-aikar, inda ya ce an samu takardun bayanan jiragen ruwa da suke satar mai zuwa kasashen waje inda za a tura kasashen da ake kai man sata daga Najeriya.
“Bincike zai ci gaba da gudana har zuwa sulusin wannan wata, har yanzu waus mutane da ke cikin gwamnati na fitar da danyen manmu ta haramtacciyar hanya. Muna kokarin samo wadannan takardu. Kuma muna samun hadin kan kasashen duniya. Kuma za mu tabbatar wadanda suke sace mai wa Najeriya sun fuskanci hukunci nan ba da jimawa ba wajen gabatar da su a gaban kotunanmu,” inji Buhari.
Ya ce, “Mun samu hadin kan wasu kasashe da ake kai danyen man, kuma muna tattaunawa da su. Za mu ci gaba da boye sirri ta yadda ba za mu fallasa ’yan Najeriya sa suke taimakawa wajen fallasa masu tallafa wa Najeriya wajen gano inda ake kai man da aka sace ba da kuma asusun ajiyar da ake shigar da kudaden cinikin maimakon na Gwamnatin Tarayya.”
Buhari ya ce gwamnatinsa tana ci gaba da nazari kan shawarwarin yadda za a sake fasalin Kamfanin Man fetur na kasa (NNPC).