Masu neman aurenmu sun guje mu saboda shiga siyasa — Matan Kwankwasiyya
Mun ba da gudunmawa sosai don ganin jam’iyyarmu ta yi nasara.
Kungiyar Matan Kwankwasiyya ta yi koken cewa manema auren ’ya’yanta sun guje su saboda shiga siyasa, lamarin da take kira ga jagororin uwar kungiyar da su dubi Allah su tsare musu mutuncinsu yayin auren zawarawa da gwamnatin Kano ta tsara yi.
Shugabar kungiyar, Shafa’atu Ahmad wacce aka fi sani da Londonbe ce ta bayyana hakan a wata tattaunawa da ta yi da gidan rediyon Freedom da ke Kano, inda ta ce tuni sun gama tantance jagororin da suke burin su aure su.
- Iraki ta kori Jakadan Sweden saboda kona Al-Qur’ani
- Kotu ta umarci DSS bai wa Nnamdi Kanu damar ganin likita
“Mun ba da gudunmmawa sosai don ganin jam’iyyarmu ta yi nasara, kuma da mu aka yi zagayen kananan hukumomin Kano 44 lokacin yakin neman zaben da aka yi.
“A cikinmu akwai ‘yan mata da zawarawa, kuma wadanda muke so su aure mu sun hada da Sanata Kawu Sumaila, Ogan Boye, dan majalisarmu mai wakiltar mazabar Albasu Dokta Ghali Albasu da sauransu.
Kan haka ne ta roki masu ruwa da tsaki na Kwankwasiyyar da su tsaya tsayin daka don ganin hakan ta tabbata, domin da gaske suke ba wai da wasa ba.
Wadannan kalamai na Shafa’atu dai ya tada kura a kafafen sada zumunta musamman Facebook, inda wasu ke ganin bakinta, wasu kuma ke ganin ta yi ne kawai don raha.
Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamnatin Kanon ta bayyana aniyarta ta dawo da tsarin aurar da zawarawa, inda za ta fara da 1,020.