Masu neman farraka Jam’iyyar APC a Kaduna ba su kishin talakawa – Aminu Shagali
Wani abu da ke damun magoya bayanku a Jihar Kaduna shi ne rikicin da ya kunno kai a jam’iyyarku ta APC inda har wadansu sun bude sabon ofishi, kuma hakan ya sa kuka kira taron masu ruwa-da-tsaki, wane karin haske za ka yi wa jama’a? Muna godiya ga Allah da Ya ba mu dama muka […]
Wani abu da ke damun magoya bayanku a Jihar Kaduna shi ne rikicin da ya kunno kai a jam’iyyarku ta APC inda har wadansu sun bude sabon ofishi, kuma hakan ya sa kuka kira taron masu ruwa-da-tsaki, wane karin haske za ka yi wa jama’a?
Muna godiya ga Allah da Ya ba mu dama muka kasance cikin masu ruwa-da-tsaki a Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna. Babban dalilin kiran wannan taro shi ne saboda a hada ’ya’yan Jam’iyyar APC a fada musu cewa yawancin mutanen nan da suke neman farraka Jam’iyyar APC ba suna yi domin al’ummar Jihar Kaduna ba ne, ba suna yi don talaka ba ne, suna yi ne domin kansu domin wani buri na kansu. Ba don cigaban al’umma suke yi ba. Abin da zai sa ka fahimci wannan shi ne yawancinsu sun mayar da ita siyasar wata hanya da za su ci wa wadansu mutunci, wata hanya da za su yi kama-karya wata hanya da za su dauka cewa babu wanda ya isa ya zama wani abu a Jihar Kaduna in ba da su ba. Sai suka dauki girman da Ubangiji ne kadai Yake da shu suka dora wa kansu. Duk mutumin da ka ga ya dauki girman Allah Ya dora wa kansa, to wannan mutum ya saurari karshensa ba zai yi kyau ba. Babu yadda za ka yi ka yi rantsuwa bisa karya, ka yi magana ka yi karya a ce kai shugaba ne. Duk mutumin da yake tunanin al’umma kullum tunaninsa shi ne idan wani matsayi yake kai yana iya yin addu’a ya ce Allah idan wannan matsayi ba alheri ba ne a gare ni da al’umma Allah Ka canja ni Ka kawo wanda zai fi ni zama alheri.
Ba ka bude baki kana cewa ku kuka kawo wani, kai din nan da ka zama abin da ka zama wa ya zamar da kai, inda za ka iya zamar da kanka da tuni ka zamar da kanka, amma sai da wani lokaci da Allah Ya kawo ta dalilin wadansu ka zama abin da ka zama.
Mai jin tsoron Allah shi ne ainihin mai tsayar da kansa a daidai matsayin da Ubangiji Ya ajiye shi ba tare da tunanin zai ci wa wani mutunci ba ko zai karya wani ko wata dama da wani mutum ke da shi ya ce yana da dalilin da zai sa shi ya rasa.
Wannan dalili ne ya sa muka hadu muka tattauna cewa wadannan da ke neman farraka al’umma kuma su farraka jam’iya ba mutanen kirki ba ne kuma ba al’umma suka sa a gaba ba kansu suka sa a gaba.
Domin sun sa bukatarsu ta wuce bukatar al’umma, wannan abu da nake fada zan iya misali ga shi mai girma Sanata mai wakiltar Shiyya ta daya. Wannan Sanata ya yi takarar Gwamna a shekarar 2003 ya yi takarar Gwamna a shekarar 2007 ya yi takarar Gwamna a shekarar 2011. Ina wannan karfi da yake tunanin zai iya ba wani yake, da bai bai wa kansa Gwamna a wannan lokaci ba?
Ina askin da yake cewa yana iya yi da bai yi wa kansa askin nan a wancan lokaci ya bai wa kansa ba. Amma da yake ya mance cewa Allah ne ke yi da Allah Ya ga dama sai a shekarar 2015 Allah Ya yi amfani da wadansu Ya ba shi kujerar Sanatan. In mutum yana da imani daga wannan lokaci zai gane shi ba komai ba ne. kashi Allah zai bar ka da shi a cikin ciki ya zama bala’i, ballantana ka je kana cewa kai ka kawo wani, babu wanda ya kawo wani sai da hukuncin Ubangiji. Dukanmu gobe Allah Yana iya kwace wannan al’amura daga hannunmu Ya bai wa wadansu, kuma dole mu gode wa Allah domin Allah a lokacin da Ya ga dama Ya ba mu ni’iimar da ba mu da ita yanzu kuma dama ce a hannunSa Ya amshe ta to masha Allah.
Wadannan dalilan suna daga cikin abubuwan da suka sa muka zauna muka kuma fada wa kanmu gaskiya. Wadanda suke kokarin farraka jam’iyya da ba su da mukamai a kore su, wadanda suke da mukamai a kyale su amma a dakatar da su na wani lokacin da za su iya fitowa fili su nuna wa al’umma cewa wadannan laifuffuka da suka yi sun janye su kuma suna son a ci gaba da gudanar da mulki yadda ya kamata. Kuma wannan farraka da suka shigo da ita sun janye ta in suka yi wannan sai a dawo da su cikin jam’iyya. Amma ba mutumin da bai yi wa al’ummar yankinsa komai ba ya zo yana cewa yana fada don talaka.
Duk mutumin da ke fada domin talaka za ka tarar da shi kullum tunaninsa talakan nan, ai akwai alawus da ake ba su da sauran kudade na yankunansu me suka yi wa al’umma a shekara biyu da rabin nan? Kuma talakan nan ne ya zabe ka kai ba wata tsiya ba ce sai ta dalilin talakan nan, amma sai ka je kana yaudarar talakan. To, talaka ya san wadanda ke yi dominsa ya san abin da ake yi a Jihar Kaduna ana yi ne domin inganta rayuwarsa. Kuma abin da muke cewa shi ne alheran da muka sa a gaba na taimakon al’iummar Jihar Kaduna Allah Ya sani dole akwai kura-kurai da za mu iya yi, amma mu a zuciyarmu muna yi ne domin Allah domin al’ummar da suka zabe mu. Ba muna yi ba ne domin kanmu, kamar ni zan iya cewa komai zan nema, nakan ce idan zan nema domin kaina ne Allah kada Ka ba ni shi. Amma duk abin da Allah zai ba ni domin al’umma su amfana da ni koda ba na sonsa Allah Ka ba ni shi.
Siyasa kada ka rika daukarta hanyar ci wa wadansu mutunci ko ka rika tunanin kana da karfin da za ka iya yi wa kanka wani abu. Dukanmu ba mu isa mu kai kanmu inda muke yanzu ba, sai da tsari na Ubangiji kuma babu abin da za mu ce wa Allah sai godiya domin Ya yi mana abin da ba mu isa mu yi wa kanmu ba. Wadannan su ne abubuwan da muka zauna muka yi hukunci a kai, kuma mun duba yadda za a yi zabubbukan kananan hukumomi.
Ko akwai wani kokari da kuka yi domin yin sulhunta ’ya’yan jam’iyyarku?
Allah da kanSa Ya ce sulhu alheri ne kuma duk mutumin da ba ya son sulhu za a iya cewa ya zama shaidani. Duk wani mutum da yake rayuwa a kullum idan aka kawo masa hanyar sulhu yana neman a zo a zauna ne a yi sulhun nan. A lokacin da ake wadannan abubuwa ba sau daya ba ba sau biyu ba na je na zauna da Gwamna na kuma zauna da wadansu da ake tunanin akwai matsala a kansu ba a gabansu ba domin a hadu a shirya a ciyar da jihar nan gaba. daya daga cikinsu ban san laifin da na yi masa ba amma sai ya dauki laifi ya dora min cewa na ki shigowa in gyara matsalolin da suke tsakaninsu da Gwamna ko da wadansu. Ni kuma a tsakanina da Allah na yi bakin iya kokarina inda shi kansa Gwamnan ya saurare ni kuma bai taba daukar wani mataki a kan wancan mutumin da yake wannan abin ba, har sai da wannan mutum ya je ya farrakar da kansa.
Babu wani mutum da zai je yana daukar abin da Allah Yake yi, ya ce shi yake yi a kyale shi. Abin da Allah Yake yi, Shi Yake yi. Siyasa kuma siyasa ce, amma duk iya siyasarka idan Allah bai ga damar za ka zama wani abu ba, ba za ka zama ba. Duk iya maganarka idan Allah bai ga damar za ka taimaki wani ya zama wani abin ba babu yadda za a yi ka zama. Mutumin da ke irin wadannan maganganu ba za mu kyale shi ba, domin mun san ba ya da wuta ba ya kuma da Aljanna, kuma ko wane ne za mu iya tsayawa mu yi fada da shi mu gaya masa gaskiya, domin mun san shi ba Allah ba ne. Allah kadai ake yi wa bauta, amma mutumin da sauro kadai in ya cije shi zai iya sanya masa cuta ne zai rika tunanin yana iya yin wani abu? Ni a tunanina idan mutum ya girma ya san ya girma,in Allah Ya fifita ka a kan wadansu ko da ba su gane ba sai ka rika fada musu gaskiya, wannan fada ne na manya wadanda suka kai wani waje.
Shi talaka da ka ce kana fada dominsa in za a zo fadan nan ’ya’yanka da matanka da ’yan uwanka na jini ba za su shigo su yi ba. Daga kai sai ’yan korenka sai wadanda kake tunanin su ba komai ba ne za ka je ka yi musu karya domin abin da kake nema.
Don haka ya kamata mu ji tsoron Allah mu guji yin duk abin da muka san ’ya’yanmu da matanmu da ’yan uwanmu makusanta su ba za su shiga wannan abu ba. kila wanda ka ce kana yi wa fada ’ya’yansa na nan ba su ci abinci ba, amma kai babu yadda za a yi ’ya’yanka su zauna ba su ci abinci sau uku ba a rana. Babu motar da ba sa hawa, kila ma a kasar waje suke karatu, amma ka ce wai kana yi wa talaka fada, akwai karyar da ta wuce wanna? Kana can kana amsar alawus dinka, kai ka san abin da kake yi da kudin, wai kai dole sai ka yi Gwamna. Alhali kila ma wanda zai zama Gwamnan a badi bai ma fito ba, kuma kila wanda yake kai a yanzu da kake fada da shi idan Allah Ya yi zai koma sai ya koma.
Idan za mu rika yin abu a siyasa mu rika fada wa mutane gaskiya, a yanzu idan mutum ya zo ya ce min mu muka yi ka, nakan ce a’a kai ba ka yini ba, ka dai zabe ni, amma Allah ne Ya hukunta zuwana wannan matsayi.
Domin a kan zabi mutum in Allah bai yi zai zama wani abu, ba kuma zai zama ba. An yi haka da yawa a lokacin jefa kuri’a kai ka ci zabe, amma sai a murde zaben nan domin Allah bai yi za ka zama ba. Amma idan Allah Ya yi sai ka zama hanyar da za a murde zaben ba za a samu ba kuma sai ka zama domin Allah Ya hukunta za ka zama.
Wane jan hankali za ka yi ga talakan da ake amfani da shi wajen ta da fitina?
Abin da zan ce da shi talaka shi ne duk wanda ya zo ya ce ka ta da fitina ka tambaye shi ina ’ya’yansa da matansa, kuma wane gida yake zaune kuma wace irin riga yake sakawa. Kai yana ba ka damar ka saka irin wadannan abubuwa da yake sa wa, kana jin dadin da shi yake ji? Ko yana yi ne saboda ra’ayin kansa? Ko kuwa dama kawai yake son ka ba shi ya je yana holewa abinsa?
Abin da yake daidaita dan talaka da dan mai kudi ko mai mulki shi ne ilimi kuma tsarin da gwamnatin jihar ta dauko shi ne a bai wa kowane dan talaka damar ya samu ilimi kamar yadda dan mai kudi ko mai mulki zai samu. Domin idan ya samu wannan dama babu yadda za a wani ya yi amfani da tunaninsa ya cutar da shi.