Masu neman mukami ne ke shirya  zanga-zanga – Buhari

Fadar Shugaban Kasa ta yi watsi da korafe-korafen da wadansu ’ya’yan Jam’iyyar APC suke yi na nuna adawa da ci gaba da tafiya da wadansu na kusa da Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban yake yi. A farkon wannan mako ne wadansu ’ya’ayn Jam’iyyar APC suka gudanar da zanga-zanga a Abuja, domin neman Shugaban da kada […]

Masu neman mukami ne ke shirya  zanga-zanga – Buhari

Fadar Shugaban Kasa ta yi watsi da korafe-korafen da wadansu ’ya’yan Jam’iyyar APC suke yi na nuna adawa da ci gaba da tafiya da wadansu na kusa da Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban yake yi.

A farkon wannan mako ne wadansu ’ya’ayn Jam’iyyar APC suka gudanar da zanga-zanga a Abuja, domin neman Shugaban da kada ya sake nada mutanen da suka ce sun “hana ruwa gudu a wa’adinsa na farko, saboda ba sa son talaka, kuma ba su da gaskiya.”

Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, ya gaya wa gidan rediyon BBC cewa wadansu masu neman mukami ne suka debo mutane domin yin zanga-zangar.

“Wadansu sun sa ido a kan wadannan mukamai saboda wasu bukatu nasu,” inji shi.

Har yanzu dai ana jiran a ga sunayen mutanen da Shugaba Buhari, ke son nadawa ministoci da mukarraban gwamnatinsa a zangon mulkinsa karo na biyu.

Masu zanga-zangar sun nuna fargaba ce kan yiwuwar Buhari ya sake tafiya da mutanen da suke zargi a wa’adin mulkinsa na biyu.

Sai dai Malam Garba Shehu ya ce, “Idan mutum ba da shi ake tafiyar da gwamnati ba, to ba abin da zai gamsar da shi.”

Ya kara da cewa ba yau aka fara irin wannan zanga-zangar ba, domin biyan bukatar wadansu, ta neman a cire wani ko a nada wani don a biya bukatunsu.Kuma masu zanga-zangar sun ce matukar aka sake nada irin wadannan mutane a mukaman siyasa to kuwa za su raba-gari da duk wasu abubuwa da suka shafi Jam’iyyar APC.

Da dama daga cikin al’ummar kasar nan da wadansu magoya bayansa na alakanta tafiyar hawainiyar da suka ce gwamnatinsa na yi da rashin zabar mutanen da suka cancanta a matsayin ministoci da sauran shugabannin muhimman ma’aikatun gwamnati.

Haka kuma ana fargabar kada a sake shafe dogon lokaci kafin a nada ministocin kamar yadda aka yi a 2015, lamarin da masana suka ce ya kawo tsaiko a harkokin mulki.

Amma Garba Shehu ya alakanta tsaikon da aka samu da hutun da majalisa ta tafi, inda ba za ta dawo ba sai a watan Yuli.

“A bari sai majalisa ta dawo an ga ba a yi nade-naden ba sannan a yi korafi, amma ba wata saba doka da tsarin mulki da aka yi ta bangaren sha’anin nade-nade,” inji shi.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos