Masu neman takarar Gwamnan Sakkwato a APC na so a yi zabe kato bayan kato
6 daga cikin masu neman takarar su 7 sun amince da bukatar
Masu neman takarar Gwamnan Jihar Sakkwato a jam’iyyar APC sun rubuta wa uwar jam’iyyar ta kasa takardar neman a yi amfani zaben kato bayan kato yayin zaben fid da gwani a Jihar.
Masu neman takarar da suka sanya hannu domin neman bukatar su ne Sanata Abubakar Gada da Ambasada Faruk Malami Yabo da Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir da Honarabul Yusuf Suleiman da Alhaji Abubakar Abdullahi Gumbi da Dakta Abdullahi Balarabe Salame.
- An haramta acaba a wasu sassan birnin Legas ‘har abada’
- Badakalar N80bn: Ministar Kudi ta dakatar Akanta-Janar, Ahmed Idris
A cikin masu neman takarar su bakwai a zaben na 2023, Honarabul Ahmad Aliyu ne kadai bai tare da wannan ra’ayin na masu neman takarar.
Sai dai duk kokarin wakilinmu na jin dalilinsa na kin tafiya tare da takwarorin nasa ya ci tura.
Honarabul Abdullahi Salame ya tabbatar wa Aminiya takardar dake yawo cewa daga wurinsu ta fito kuma duk wanda sunansa ya bayyana a takardar ya aminta da a nemi wannan bukatar ga uwar jam’iyar APC.
Ya ce, “Takardar gare mu ta fito domin muna son abai wa kowa damarsa ta zama dan jam’iyya, duk abin da Allah ya yi za mu karbe shi.
“Mu duka ’yan takarar shida mun gamsu da a yi zaben kato bayan kato da fatan uwar jam’iyya za ta duba kokenmu”, a cewar Salame.
A cikin takardar da suka rubuta, ’yan takarar sun nuna kan shari’ar da ake yi a Sakkwato ta shugabanci yakamata a duba bukatarsu.
In ba a manta ba, tun bayan kammala zaben shugabannin jam’iyar ne a Jihar bangaren Salame da Abubakar Gada suka kalubalanci tsagin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a kotun Abuja, inda da aka yi ta tirka-tirka ba a kammala ba, kowane bangare na kiran kansa shi ne halastaccen shugaban jam’iya.
Ranar Laraba ce dai ake sa ran kammala shari’ar a inda Alkalin Babbar Kotun Tarayyar da ke Sakkwato zai yanke hukunci kan dambarwar da ta ki ci ta ki cinyewa.