… Masu neman takardar makarantata za su tabbata a kotu – Buhari

dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya ce kamata ya yi ’yan Najeriya su saurari Hukumar Zabe ta kasa (INEC) maimakon yawan surutu kan ingancin takardar makarantarsa. Janar Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai bayan ganawa da shugabannin Jam’iyyar PDM wadanda suka gabatar masa […]

… Masu neman takardar makarantata za su tabbata a kotu – Buhari
… Masu neman takardar makarantata za su tabbata a kotu – Buhari

dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari ya ce kamata ya yi ’yan Najeriya su saurari Hukumar Zabe ta kasa (INEC) maimakon yawan surutu kan ingancin takardar makarantarsa.

Janar Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai bayan ganawa da shugabannin Jam’iyyar PDM wadanda suka gabatar masa da matsayarsu ta goya masa baya a zaben Shugaban kasa da za a gudanar a ranar 14 ga watan Fabrairu mai zuwa.
Ya ce Hukumar INEC ta samu takardunsa, inda ya ce duk wanda yake da wani ra’ayi na daban yana iya zuwa kotu don a bi masa kadi.
“Ba zan ji mamaki ba, wannan Najeriya ce. Idan mutane da gaske suke yi kan wannan batu, sai su saurari Hukumar INEC. Na tsaya takarar wannan mukami, wannan ne karo na hudu. Hukumar INEC bias doka ta samu wadannan takardu, sun ce eh sun same su; don haka duk wanda yake da wani ra’ayi sabanin haka ya tafi kotu. Yanzu suna kotu, to a kyale su su yita zama a can,” inji Buhari.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ganawar, Shugaban Jam’iyyar PDM ta kasa, Alhaji Bashir Ibrahim, ya musanta cewa sanya hannun Atiku Abubakar ko tilastawarsa ce ta sanya jam’iyyarsa ta goyi bayan dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar APC.
“Babu wanda aka yarda ya kasance dan jam’iyyar siyasa biyu. Atiku ya tsaya takarar neman Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC ne; don haka wannan ba zai yiwu ba,” inji Bashir Ibrahim.
Tuni wani lauya mazaunin Abuja Mista Chike Okafor ya bukaci Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta haramta wa Buhari tsayawa takara a zaben Shugaban kasa na 14 ga Fabrairu bias zargin bayar da bayanin karya.