Masu neman wargaza Najeriya sun jahilci manufar Allah game da ita – Dogara
Labarai daga Salihu Maqera Shugaban Majalisar Wakilai Barista Yakubu Dogara, ya ce waxanda suke kiraye-kirayen a wargaza Najeriya ba su san shirin Allah game da qasar nan ba. Dogara ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen addu’ar nuna godiya a cocin His Elect Christian Assembly Church da ke Nyanya, Abuja, a ranar […]

Labarai daga Salihu Maqera
Shugaban Majalisar Wakilai Barista Yakubu Dogara, ya ce waxanda suke kiraye-kirayen a wargaza Najeriya ba su san shirin Allah game da qasar nan ba.
Dogara ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a wajen addu’ar nuna godiya a cocin His Elect Christian Assembly Church da ke Nyanya, Abuja, a ranar Lahadin da ta gabata, inda ya ce, kafuwar Najeriya ba kuskure ba ne, domin Ubangiji wanda Ya qirqiro qasar Yana da kyawawan tsare-tsare ga al’ummarta.
“Waxanda suke tunanin kasancewa Najeriya qasa kuskure ne, mia yiwuwa saboda ba su san manufar haka ba ne. Kuma idan kana so ka san manufar abu, sai ka koma baya ka bi diddigi ka daddale abubuwa. Aikin wanda Ya halitta ta ce, don haka ina qalubalantarsu su koma baya zuwa ga wanda ya halicci Najeriya, Shi ne Ubangiji domin mu gano abin da ya shafi Najeriya.”
Ya qara da cewa: “Inda muka yi kuskure ta yiwu a lokacin Yaqin Basasa ne, wannnan qasa tana iya wargajewa amma Allah Ya bar ta a dunqule, Ubangiji bai tava yin kuskure ba.”
Shugaban Majalisar ya ce tunda qasar nan ta tsallake Yaqin Basasa hakan yana nufin akwai wata manufa ga qasar, kuma “Idan ba a cimma makomar qasar nan ba, babu abin da zai faru da Najeriya,” inji shi.
Ya amince cewa Najeriya tana fuskantar matsaloli da dama, sai dai ya buqaci ’yan Najeriya da kada su gajiya wajen yi wa qasar nan addu’o’I, inda ya ce babu abin da Ubangiji ba zai iya yi ba, ciki har da warware matsalolin Najeriya.
“Ba za mu daina yi wa qasarmu addu’o’i ba, musamman mu taru mu yi addu’a. Dukanmu mun san amfanin a haxu a yi addu’a; an ce duk lokacin da mutum biyu ko uku suka haxu suka roqi wani abu, Ubangiji zai amsa. Mun san qalubalen da muke fuskanta, qalubale masu yawa masu wahala, amma za a iya kawar da su. Idan Allah Ya kasance tare da mu za mu magance su, kuma har da kawai za mu yi haka, ita ce idan muka samu hikimar Ubangiji; hikima na nufin yin aiki da ilimi,” inji Dogara.
Tun farko a huxubarsa, babban faston coci, Salem Salako-Saja, ya yi wa’azi ne kan yadda Baibul ke kusatar da mutum ya samu yalwa a iyalinsa, inda ya buqaci mahalarta su rungumi zaman lafiya a tsakanin iyalai da kuma matakin qasa.
Fasto Salako-Saja ya kuma jagoranci yin addu’o’i na musamman ga qasar nan domin ta samu fita daga matsalolinta.