Masu ruwa-da-tsaki sun yi taro kan Tashar Teku-Huta ta Kaduna

Masu ruwa-da-tsaki sun gudanar da taro kan Tasher Teku-Huta ta Kaduna a otel din Federal Palace da ke Tsibirin bictoria Island da ke Legas a ranar 24 ga Janairun bana. A lokacin taron, Babban Sakatare kuma Shugaban Gudanarwar Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), Barisat Hassan Bello ya bukaci masu ruwa-da-tsaki su hada hannu […]

Masu ruwa-da-tsaki sun yi taro kan Tashar Teku-Huta ta Kaduna


Masu ruwa-da-tsaki sun gudanar da taro kan Tasher Teku-Huta ta Kaduna a otel din Federal Palace da ke Tsibirin bictoria Island da ke Legas a ranar 24 ga Janairun bana.

A lokacin taron, Babban Sakatare kuma Shugaban Gudanarwar Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), Barisat Hassan Bello ya bukaci masu ruwa-da-tsaki su hada hannu wajen cimma burin kafa Tashar Teku-huta ta ta Kaduna.

Barista Bello ya ce hada hannu a tsakanin masu ruwa-da-tsaki zai taimaka wa Gwamnatin Tarayya wajen saukake harkokin kasuwanci a tashoshin Teku Huta na kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci dukan masu ruwa-da-tsaki su hada kai don cimma nasarar ayyukan tashoshin Teku-Huta da suke kasar nan.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Shugaban Tashar Teku-Huta ta Kaduna, Mista Tope Borishade da Manajin Daraktan Hukumar Jiragen kasa Mista Fidelis Okhiria da Mataimakin Kwanturolan Hukumar Kwastam, Musa Manniru da sauransu.