Masu safarar hodar iblis da kan mutane sun shiga hannu
Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta yi nasarar kame mutane uku da ake zargi da safarar hodar iblis (cocaine) da kan mutane a yankin Ayetoro da ke jihar. A cewar kakakin ‘yan sandan jihar ASP Abimbola Oyeyemi Mutanen da ake zargin sun hada da Sha’aibu Popoola da Aliu Ajiroba sai Jimoh Ijiola. Da fari dai […]
Rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun ta yi nasarar kame mutane uku da ake zargi da safarar hodar iblis (cocaine) da kan mutane a yankin Ayetoro da ke jihar.
A cewar kakakin ‘yan sandan jihar ASP Abimbola Oyeyemi Mutanen da ake zargin sun hada da Sha’aibu Popoola da Aliu Ajiroba sai Jimoh Ijiola. Da fari dai jami’an ‘yan sandan da ke sintiri ne suka tare Popoola da Akibora a lokacin da suke kan babur kirar Bajaj dauke da wani buhu, wanda ‘yan sanda ba su aminta da shi ba, nan take suka nemi su bude shi, inda aka samu hodar iblis da kan mutum biyu a ciki. Nan take suka kame su kana suka tasa keyarsu zuwa ofishin ‘yan sanda da ke yankin Ayetoro, inda suka ce Jimo Ijiola ne ya ba su kokon kan bayan da jami’an ‘yan sandan suka kamo shi sai ya musanta alakar shi da kokon kan.
Wadanda ake zargin sun bayyana cewa, daga kasar Benin suka yo safarar kokon kan da zimmar yin tsafin kudi da su.
Kwaminshinan ‘yan sandan Jihar Ogun Ahamad Iliyasu ya ba da umarnin tasa keyarsu zuwa sashen binciken manyan laifuka na rindunar kafin daga bisani a gurfanar da su a gaban kotu.