Masu safarar shinkafa sun kashe jami’in Kwastam a Ogun

Wasu da ake zargin masu safarar shinkafa ne daga wasu kasashe, sun kashe wani jami’in Kwastam da raunata wani a unguwar Asero a Abeokuta babban birnin jihar Ogun. Rahotanni na bayyana cewa, Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya, kwastam reshen jihar Ogun sun ce, a wani sintiri da jami’an suke a hanyar unguwar Asero akan dakile […]

Masu safarar shinkafa sun kashe jami’in Kwastam a Ogun

Wasu da ake zargin masu safarar shinkafa ne daga wasu kasashe, sun kashe wani jami’in Kwastam da raunata wani a unguwar Asero a Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Rahotanni na bayyana cewa, Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya, kwastam reshen jihar Ogun sun ce, a wani sintiri da jami’an suke a hanyar unguwar Asero akan dakile shirin safarar kaya ranar Lahadi .

An kashe jami’in hukumar Kwastam Hamisu Sani da ne lokacin da raunata sufeta Tijjani Michel lokacin da suke kokarin binciken motoci takwas da aka yi safarar shinkafa aka ajiye a unguwar Asero.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta