Masu samar wa ’yan Boko Haram miyagun kwayoyi sun shiga hannu – Sojoji

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta da ke aikin dawo da zaman lafiya a Jihar Borno da sauran jihonin Arewa maso Gabas sun kama wasu mutane da miyagun kwayoyi da kuma tabar wiwi a cikin wata mota a garin Geidam na Jihar Yobe a ranar Talatar da ta gabata.Rundunar ta yi zargin cewa mutanen ne […]

Masu samar wa ’yan Boko Haram miyagun kwayoyi sun shiga hannu – Sojoji
Masu samar wa ’yan Boko Haram miyagun kwayoyi sun shiga hannu – Sojoji

Rundunar Sojin Najeriya ta ce dakarunta da ke aikin dawo da zaman lafiya a Jihar Borno da sauran jihonin Arewa maso Gabas sun kama wasu mutane da miyagun kwayoyi da kuma tabar wiwi a cikin wata mota a garin Geidam na Jihar Yobe a ranar Talatar da ta gabata.
Rundunar ta yi zargin cewa mutanen ne ke kai wa mayakan kungiyar Boko Haram man fetur da miyagun kwayoyi irin su wiwi da madarar sukudaye da kuma taramol.
Kakakin Rundunar Sojin kasa ta Najeriya, Kanar Sani Usman Kuka-Sheka, ya ce sojoji sun kama mutanen ne a wurin binciken abubuwan hawa a hanyar Dapchi zuwa Gaidam.
Ya ce sun yi nasarar kama mutanen ne bayan umarnin da hedikwatar tsaro ta bayar ga sojoji cewa su kara kaimi wajen binciken abubuwan hawa a yankin Arewa maso Gabas.
A makon jiya Kanar Kuka-Sheka ya fadi a shafinsa na Facebook cewa ’yan Boko Haram da dama da sojojin Najeriya suka kama ba su iya karanta koda Fatiha daga Alkur’ani ba, amma suke da’awar kafa “Daular Musulunci.”
Ya ce, “Lokacin da sojojin Najeriya suka kama sansanoni da wuraren atisayen ’yan Boko Haram ba su iske Alkur’ani ko wani littafin addinin Musulunci ba, amma sun iske harsasai da layu da kwaroron roba da sauran kwayoyin magunguna ciki har da masu kara kuzarin jima’i.”
Sai ya kara da cewa: “Don haka muna rokon jama’a su ci gaba da ba mu goyon baya da hadin kai. Kuma muna maraba da duk wani bayani da zai taimaka wajen kamo ’yan Boko Haram ko dakile mugun shirinsu da sauran miyagun da ke cikin al’umma.”