Masu sana’ar fatu na asarar Naira biliyan uku saboda amfani da gishiri – Yahaya Kura
Alhaji Yahaya Kura shi ne manajan da ke kula da shirin Gems 4 a Jihar Kano, a tattaunawarsa da Aminiya ya ce shirin Gems 4 ya dauki harkar fatu ne don magance dimbin asarar da masu wannan sana’a ke tafkawa ta hanyar ajiyar fatu. Kuma ya nuna yadda ya kamata gwamnati ta bi wajen tallafa […]
Alhaji Yahaya Kura shi ne manajan da ke kula da shirin Gems 4 a Jihar Kano, a tattaunawarsa da Aminiya ya ce shirin Gems 4 ya dauki harkar fatu ne don magance dimbin asarar da masu wannan sana’a ke tafkawa ta hanyar ajiyar fatu. Kuma ya nuna yadda ya kamata gwamnati ta bi wajen tallafa wa masu sana’ar fata a kasar nan:
Aminiya: Mene ne manufar wannan shiri na Gems 4?
Yahaya Kura: Gems 4, wani shiri ne a karkashin Hukumar Raya kasashe ta Birtaniya (DFID) da Bankin Duniya. Shiri ne da yake da burin taimaka wa jama’a a cikin sana’o’insu, musamman a harkar da ba ta da nasaba da man fetur. Ana so ne a bunkasa harka mai dorewa da jama’ar kasa za su dogara da ita. Hakan ya sa ake zabar muhimman fannonin kasuwanci domin a taimaki masu yin su. Yadda muke aikinmu shi ne da farko za mu fara nazartar sana’a mu ga abin da ta kunsa. Yawanci mukan duba inda matsaloli suke sai mu yi kokarin zakulo su tare da neman hanyar magance su domin a samu ci gaba a sana’ar. A yanayin haka ba mu daukar aiki da yawa, ma’ana mun fi so mu dauki matsala daya ko biyu, domin a samu tasirin aikin. Haka wanann aiki da muke yi kyauta ne ba a karbar ko kwabo daga masu sana’o’i, ma’ana tallafi ne daga kasar Birtaniya ga mutanen don bunkasa sana’o’i.
Aminiya: Me ya ja hankalinku kuka zabi harkar fata?
Yahaya Kura: Da muka zo aiki a nan sai muka zabi harkar fatu da kiraga. Mun gano cewa harkar fata ita ce ta fi kowace sana’a samar wa kasar nan kudin shiga baya ga man fetur. Duk shekara Najeriya tana samun kimanin Dala miliyan 600 daga harkar fata, shi ya sa muka dauki harkar fata. A bincikenmu mun gano cewa masu wannan harka suna tafka asara mai yawa wajen ajiyar fatu kafin mika su ga majema.
Daga lokacin da aka yanka dabbobi a gida ne ko a kwata, fatun sukan shiga yanayi daban-daban. Fata danyar kaya ce ana cire ta daga jikin dabba za ta fara lalacewa. Yawanci ba ta daukar fiye da mako guda ba lalace ba. Gashi kuma duk fadin kasar nan a Jihar Kano ne kadai ake da kamfanonin jima, hakan ya sa fatun sai sun zo Kano daga jihohin kai har da kasashen makwabtanmu. Sai ya zama masu harkar fatun suna asara mai yawa kafin su iso ga majema. Sai muka ce bari mu duba yadda za mu magance wa masu wannan sana’a matsalar ajiya da yadda za su alkinta fatun su kai ga masaya ba tare da sun lalace ba, don ganin masu sana’ar ba su yi asara ba tare da ganin sun samu riba mai yawa. A bincikenmu sai muka gano a Najeriya masu harkar fata suna amfani da gishirin da ake miya wajen ajiyar fatu, alhali ba shi ne gishirin da ya dace da ajiyar fatu ba, akwai gishirin ajiya na musamman da aka yi domin fatu, wanda yake dauke da sinadaran da ke hana abubuwa lalalcewa. Kuma da irin wannan gishiri kasashen duniya ke amfani wajen ajiya, don haka sai muka yi kokarin samo wa masu harkar wannan gishiri inda muka sayo shi daga kasar Jamus da niyyar kawo shi kasuwar kasar nan ya maye gishirin da ake amfani da shi a wanda don miya aka yi shi. Manufarmu ita ce idan mun ga ya karbu sai mu yi kokarin ganin ana yin sa a kasar nan.
Da muka kawo wannan gishiri sai muka nemi hadin kan kungiyoyin masu harkar fata inda suka tara mana mamboninsu muka wayar musu da aki game da shirin da muka zo da shi. A nan ne muka gudanar da aikin gwaji a cibiyoyin da ake ajiyar fatu a Jihar Kano. Yadda muka yi shi ne muka samu fatu masu kyau sosai sai muka raba biyu; kashi na farko muka sanya mata gishirin da ake ci, daya kashin muka sanya wannan gishiri na ajiya. Muka ajiye su a wuri guda muka diba musu wa’adin mako uku. A makon farko duk fatun biyu suna nan lafiya lau. Amma da aka yi mako biyu zuwa uku sai muka samu waccan fatar da aka sanya wa gishirin da ake ci ta lalace yayin da wadda aka sanya wa gishirin ajiya babu abin da ya same ta. Saboda ba zai yiwu mu ci gaba da kawo wannan gishiri daga kasar waje ba, sai muka yi kokarin hadin gwiwa da kamfanin dangote inda ya yarda zai yi mana gishirin ajiyar. Da suka yi gishirin suka kawo mana sai muka gwada muka ga yana aiki kamar yadda wancan yake yi, don haka muka amince musu su ci gaba da samar da gishirin.
Aminiya: Zuwa yanzu yaya za ka auna karbuwar gishirin a wurin masu harkar fata?
Yahaya Kura: Tun lokacin da muka gudanar da gwajin wannan gishiri jama’a suka ga aikinsa sai suka karbe shi hannu bibbiyu, inda muka rika ba su gishirin kyauta. Amma duka da haka akwai aiki a gabanmu wajen ganin mun ci gaba da wayar wa masu sana’ar kai a sassan kasar nan, don su gane muhimmancin gishirin na ajiya. Kin san sabon abu karbuwarsa sai an yi aiki kwarai da gaske. Amma duk da haka yanzu akwai ci gaba, kullum mutane suna kara gane amfanin gishirin ajiya, tare da daina amfani da gishirn da ake ci a harkar fata. Masu sayen fata sun fi son mai kyau, don haka suka kasa ta kashi-kashi ta yin la’akari da darajarta. Akwai lamba daya da lamba biyu da lamba uku da kuma zare, wato marar kyau. Kowace da kudinta; ga misali idan mai lamba daya ana sayenta Naira dubu daya, lamba biyu kuma za a saye ta Naira 600, yayin da lamba uku za a saye ta Naira 400. Ita zare kuwa ba za ta wuce Naira 200 ba. Don haka mai sayen fata sai ya caje ta sosai don kada ya sayi asara.
kiyasinmu ya nuna cewa a Najeriya ana samun fata kamar miliyan 50 wanda a cikin wannan adadi ana samun fata miliyan biyar da suke lalacewa sakamakon ajiya da gishirin da ake ci. Ke nan akalla ana asarar
Naira biliyan uku duk shekara. Shi ya sa muke wannan aiki domin mu ga mun taimaka an mayar da waccan asarar da suke yi ta zama riba. Ina amfani da wannan dama wajen yin kira ga masu sana’ar fata su fahimci alherin da ke cikin wannan shiri su yi kokrin daina yin amfani da gishirin da ake ci su yi da gishirin ajiya. A yanzu haka muna kokari mu ga kamfanonin da za su samar da gishirin nan sun samar da shi da araha don masu sana’ar su samu sauki.
Aminiya: Wane kira kake da shi ga gwamnati don ganin ta tallafa wa masu harkar fatu?
Yahaya Kura: Kira ga gwamnati shi ne ta shigo cikin masu harkar nan domin ta fahimci matsalolinsu. Mun lura cewa duk da kudin shiga da gwamanti ke samu daga masu wannan harka har yanzu babu wani tallafi da suke samu daga gare ta. Kamar gwamnati ba ta san da su ba. Sana’ar fatu ba ta da matsalar kasuwa sai dai matsalar ajiya. Akwai bukatar gwamnati ta tallafa wa masu harkar ta bangaren samar musu da wadataccen gishirin ajiyar a kan farashi mai rahusa. Kuma gwamnati ta shigo ciki wajen samar musu wuri na musamman da za su rika gudanar da sana’arsu maimakon yadda suke a warwatse a yanzu. A yi musu wata cibiya ta fatu, musamman saboda muhimmancin da ke cikin harkar fata. Abin da mutane ba su sani ba shi ne fatar Najeriya tana da daraja kwarai a duniya. Saboda haka akwai bukatar gwamnati ta kara inganta harkar don sama wa kasar nan mafita, musamman a wannan lokaci da darajar man fetur ke faduwa a kasuwar duniya.