Masu sana’ar gawayi ke kai wa ’yan bindiga bayanai —Basarake
Kamen da sojoji suka yi a yankin ya nuna cewa masu gawayin ne kashi 75% na mutanen da ke kai wa ’yan bindiga bayanai
Wani basarake a yanin Kachia da ke Jihar Kaduna ya zargin masu sana’ar gawayi a yankin da kai wa ’yan bindiga bayanan sirri.
Basaraken, wanda ya nemi a boye sunansa ya ce kamen da sojoji suka ya yi a yankin ya nuna cewa masu gawayin ne kashi 75% na mutanen da ke kai wa ’yan bindiga bayanai.
A hirarsa da wakilinmu ta wayar tarho a ranar Litinin, basaraken ya bayyana cewa galibin masu harkar gawayin suun zama ’yan aiken ’yan bindiga.
- Dangote da BUA za su gurfana a majalisa kan badakalar haraji
- EFCC ta gayyaci shugaban hukumar aikin Hajji kan N90bn
A cewarsa, ’yan bindigar sukan gindaya wa masu gawayin sharadi kafin su bar su su gudanar da sana’arsu a dazukan da ke yankin.
“Sharuddan sun hada da sayo musu kayan abinci da miyagun kwayoyi da sauran bukatu da kuma kawo bayanai ga ’yan bindigar.
“A wadannan dazuka da nake magana, babu manomin da ya isa ya je ya noma gonarsa, amma masu sana’ar gawayin suna zuwa su yi harkokinsu yadda suka saba,” in ji shi.
Kokarinmu na samun karin bayani daga kakakin rundunar ’yan sadana a Jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, bai yi nasara ba.
Har har aka kammala wannan labarin jami’in bai ba da amsar sakon da muka aike masa ba kan wannan zargi.