Masu satar fasaha suna cutar da al’umma

Sanin kowane a halin da muke ciki masana’antun da ke sarrafa fina-finai da na marubuta na matukar kokawa a kan yadda ake yi musu karan-tsaye a harkarsu inda suka ce ana matukar kawo masu ci- baya a harkar. Na dauka masu yin wannan harka suna yi ne don samun abin da za su saka ga […]

Masu satar fasaha suna cutar da al’umma
Masu satar fasaha suna cutar da al’umma

Sanin kowane a halin da muke ciki masana’antun da ke sarrafa fina-finai da na marubuta na matukar kokawa a kan yadda ake yi musu karan-tsaye a harkarsu inda suka ce ana matukar kawo masu ci- baya a harkar.

Na dauka masu yin wannan harka suna yi ne don samun abin da za su saka ga bakin salati, domin kuwa masu kokawa da wannan mummunar dabi’ar suna yi ne ganin yadda  suke kashe makudan kudi wajen fitar da fim a tsadance amma kafin fim din ya fito sai ka ga an sauke shi ta yanar gizo ana yada shi ta waya.

Ko kuma ka ga an dunkule fina-finai da dama a manhaja daya (DBD) ko ka je kasuwanni ka ba da ’yan kudin da ba su taka kara ba a tura maka a wayar hannu ta yadda za ka ga ta nade fina-finai masu yawa wanda hakan na sanya su yi asarar abin da suka kashe domin kuwa duk fim din da suka sa a kasuwa ba za su yi ciniki ba.

Haka yake ta bangaren marubuta sai ka ga an sanya littafi a zaurukan kafafen sadarwa wanda hakan zai fi yi wa masu karatu saukin samu da karantawa.

Sai kuma wata satar fasahar da ta zama ruwan dare wadda take illa ga tunaninmu zuwa ga al’adunmu da addininmu da sauran al’amurran rayuwarmu ita ce ta satar fasaha a kafar sadarwar sada zumunci (Piracy in social media)

1- Wannan ko shakka babu yakan raunana tunanin al’umma ta yadda za ka ga mutum bai iya sarrafa kwakwalwar da Allah Ya ba shi don fitar da abin da zai amfani al’ummarsa.

2- Yana sanadiyar yaduwar labaran kanzon kurege don kuwa mai daukar irin wadannan labarai yana turawa bai da ingancin gaskiyar labarin sai ka ga ana yawo da karairayi a cikin al’umma.

3- Cin fuskar addini ta yadda za ka ga kowa ya zama malami yana karantarwa gami da ba da fatawa, ko kuma ka ga ana yawo da zantukan da ba su da tushe balle makama ana alakanta su da addini ko a ce daga bakin da ba ya karya ko sanya sharudda ga duk wanda ya samu sakon wanda rashin kiyaye su na iya ja wa mutum asara, duk wannan ka ga bai da alaka da addini.

4- Yada zantuka na badala ko labarai masu cin zarafin wani jinsi ko yare ko addinin Musulunci kuma babban takaicin cikin ’yan dakikai sai ka ga har rige-rige ake yi don yada zantukan kai ka ce wasu makudan kudi aka alkawarta ga duk wanda ya tura da wuri.

5- Yawo da batanci da cin fuska kai har da zagi ga shugabanni wanda wani ne zai zauna ya shirya kage ko cin fuska sai kuwa ka ga ana yamadidi da shi kai ka ce wata aya ce.

Tunatarwa:

1- Don mutum ya dauki abin da zai amfanar da al’umma da kasa baki daya ba laifi ba ne, inda abin yake zama abin zargi shi ne ta yadda mutum zai dauki abin da bai san ingancinsa ba ko wani batanci yana yawo da shi wanda da za a turke shi a kan ya kawo hujjar aikata hakan sai ka ga yana raba na mujiya.

2- Ko shakka babu duk wanda zai zauna ya zurfafa tunaninsa kuma ya bata lokacinsa ko dukiyarsa sannan a samu wani cikin kankanen lokaci ya kwashe wannan fasaha dole ne ya ji zafin hakan kuma in har abin ya jibinci dukiyarsa zai iya daukar matakin shari’a a kan kowane ne.

Shawara:

1- Ga duk wanda yake son yada wani abu mai mahimmanci in yana da kusanci da wanda ya rubuta abin ya yi kokarin neman izininsa kuma na tabbata in har abin na karuwa ne ba zai hana shi ba.

2- In har ba ka da hanyar tuntubar mai wannan fasaha ko karantarwar in malami ne kuma ka tabbatar da ingancin abin da ya rubuta ko tababa babu zai amfani al’umma sai ka yada shi da sunan wanda ya rubuta in ma ya sa lambar waya ka rubuta lambar wanda in ma har akwai wani abu na kuskure kowa ya san ba kai ka rubuta shi ba.

Kira:

Kira na ga al’umma shi ne mu kasance masu amfani da kwakwalwar da Allah Ya ba mu domin sarrafata ta yadda za ta amfani al’ummar da muke wakilta.

Allah Ya amfanar da mu da abinda na  fada in kuma akwai kuskure a ciki saboda karancin fahimta sai a tuntube ni ta kyakyawar fuska don gyarawa.

Sanusi Hashim (Abban Sultana)

Mai sharhi ne a kan al’amurran  yau da kullum  daga Jihar Katsina [email protected], 08065507271