Masu satar kudin jama’a ta katin ATM a bankuna sun shiga hannu

Dubun wasu matasa da suka kware a wajen sata a bankuna ta amfani da katin ATM a na’urorin cire kudi na bankuna ta cika, bayan da suka fada hannun ’yan sanda a garin Katsina. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Katsina Muhammed D. Hurdi ya shaida wa manema labarai a ofishinsa yayin gabatar da wadanda ake zargi […]

Masu satar kudin jama’a ta katin ATM a bankuna sun shiga hannu
Masu satar kudin jama’a ta katin ATM a bankuna sun shiga hannu

Dubun wasu matasa da suka kware a wajen sata a bankuna ta amfani da katin ATM a na’urorin cire kudi na bankuna ta cika, bayan da suka fada hannun ’yan sanda a garin Katsina.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Katsina Muhammed D. Hurdi ya shaida wa manema labarai a ofishinsa yayin gabatar da wadanda ake zargi a ranar Litinin cewa, wadanda ake zargin wato Omotayo Bamidale da ke zaune a Garki, Abuja da Akura da ke zaune a Benin Jihar Edo an kama su ne a ranar 15/9/14 da misalin karfe 8:00 na dare a lokacin da suka bar jakkunansu a cikin motar hayar da suka shiga a bakin Tsohuwar Tasha inda suka tunkari daya daga cikin bankunan da ke wurin don aiwatar da aikin da ya kawo su.
Ya ce fasinjojin da ke cikin motar ne hankalinsu ya tashi ganin cewa an bar musu jakkunan da ba su san abin da ke cikinsu ba, nan take suka fara kururuwar da ta sa aka kama mutanen aka mika su ga jami’an tsaron.
Kwamishinan ya ce, da aka bincike su an samu katunan ATM 33 na bankuna daban-daban da na’urar kwamfuta ta hannu da kuma Naira 500.
Ya ce da aka tuhume su, sun ce sun zo Katsina ne da nufin kwashe kudin wata mace ne (an sakaya sunanta) da aka turo daga kasar Uragay, sun ce a nan ne suke ganin za su iya fitar da kudin da ba a bayyana yawansu ba a cikin tsanaki.
Kwamishina Hurdi ya ce, jami’ansa sun yi nasarar kama mutum 55 da ake zargin barayin shanu ne da ke da maboya a Dajin Rugu wadanda suka addabi yankunan Jibiya da Batsari zuwa kankara da sauransu, inda jami’ansa suka yi nasarar kwato shanu 218 da tumaki 99 da babura 8 tare da wata mota da ake zargin da ita suke amfani wajen daukar dabbobin. Kwamishina Hurdi ya ce, daga watan Agusta rundunarsa ta yi nasarar kama ’yan fashi 7 da motoci 7 da ake zaton ’yan fashin sun kwace su daga jama’a cikinsu har da wata mai fentin taksi na Abuja, kuma tuni wasu suka karbi motocinsu bayan an tabbatar da
shaidar mallakarsu.
Daga cikin wadanda rundunar ta kama har da wasu matasa uku a garin Funtuwa da ake zarginsu da aikata luwadi. daya daga cikinsu mai suna Usman Aliyu mai shekara 18 ya shaida wa ’yan sandan cewa wani mai suna Malam Magaji Aliyu dandume ke daukarsu yana amfani da su.
Da Aminiya ta tuntubi Magaji Aliyu dandume ya ce Shaidan ne ya rude shi ya aikata laifin da ake zarginsa na luwadi da yaran, inda ya yi nadamar aikata hakan.  

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi