Masu satar kudin mutane ta banki sun shiga hannu

Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta kama mutum 10 da ake zargin sun kware wajen sace kudaden mutane daga ajiyar bankunansu ta hanyar satar lambobin wayarsu. Da yake gabatar da mutanen maza 9 da mace daya ga ’yan jarida a Ibadan, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Mista Shina Olukolu ya ce, Manajan Harkokin Tsaro na Kamfanin […]

Masu satar kudin mutane ta banki sun shiga hannu

Kabir Yayo Ali, Ibadan

Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta kama mutum 10 da ake zargin sun kware wajen sace kudaden mutane daga ajiyar bankunansu ta hanyar satar lambobin wayarsu.

Da yake gabatar da mutanen maza 9 da mace daya ga ’yan jarida a Ibadan, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Mista Shina Olukolu ya ce, Manajan Harkokin Tsaro na Kamfanin Airtel, Mista Adeniyi Ige ne ya je hedkwatar ’yan sandan dauke da bayanan koke-koken sace kudi daga ajiyar bankunan mutanen da kamfanin ke hulda da su.

Shugaban Sashen Nazarin Ilimin Dabbobi na Jami’ar Ibadan Farfesa Olapade James ya kai irin wannan kuka na sace Naira dubu 180 daga ajiyar bankinsa, yayin da wani mai suna Godwin Unigbe ya ce an sace masa Naira miliyan 3 daga ajiyar bankinsa ba tare da saninsa ba. Sai Benjamin Udo Bassey wanda ya ce an janye Naira dubu 460 daga ajiyar bankinsa. Dukkan sace-sacen an gudanar da su ne cikin watan Fabrairun bana , inji Kwamishinan.

A wani binciken cikin gida da Kamfanin Airtel ya gudanar ta hanyar kyamar CCTB ya gano ma’aikata 3 da ke aiki a kamfanin ISON BPO masu suna Omotayo Azeez da Olufade Abdulgafar da Shiyanbola Harry da hannu a cikin wannan lamari, inda aka kama su. A ci gaba da bincike da rundunar ’yan sandan ta gudanar ne ya sa aka yi nasarar kama sauran mutum 7 da suka hada da tsohon ma’aikacin bankin Union Bank, Effiog Udofia mai shekara 52 da Arowosegbe Adewale mai shekara 43 da Adesina Peter mai shekara 32 da Odugbesan Gbenga mai shekara 39 da Adesanlu Kayode mai shekara 32 da Onasile Abiola mai shekara 25 da wata mace mai suna Temitope Fatai mai shekara 21. Dukkansu ba su musanta laifin da ake zargin sun aikata ba, inji Kwamishinan.

Binciken da ’yan sanda suka gudanar ya nuna cewa mutane suna sace lambobin wayar mutane ne da suke kiran layukan wayar mutanen da suke yi musu bayanan sirri tare da sace dukkan bayanan kudin ajiyar banki na mutanen da suke janye kudadensu ba tare da saninsu ba. Bullar wannan sabon salon damfara ne ya sa Kwamishinan ya yi kira ga jama’a su yi taka-tsantsan wajen amsa bayanan da irin wadannan mutane suke nema a lokacin da suka kira layukan wayoyinsu. Sannan ya tabbatar da cewa za a hanzarta gurfanar da wadannan mutane a gaban kotu da zarar an kammala bincike.