Masu satar shanu sun koma garkuwa da mutane a Kaduna
Mutanen da ake zargi da satar shanu a wasu yankunan Jihar Kaduna sun koma yin garkuwa da mutane domin daukar fansa, inda a ranar Lahadin da ta gabata al’ummar Tsohon Yadin Kamfanin UAC da ke kauyen Gyallo da kuma na Jeka-Da-Kolo da Turnuku suka wayi gari an sace musu wasu fitattun mutanensu biyu. Mutanen da […]
Mutanen da ake zargi da satar shanu a wasu yankunan Jihar Kaduna sun koma yin garkuwa da mutane domin daukar fansa, inda a ranar Lahadin da ta gabata al’ummar Tsohon Yadin Kamfanin UAC da ke kauyen Gyallo da kuma na Jeka-Da-Kolo da Turnuku suka wayi gari an sace musu wasu fitattun mutanensu biyu.
Mutanen da aka sace su ne, Alhaji Hamisu Usman mai kimanin shekara 52 da Ibrahim Luna mai shekara 41 wadanda dukkansu suna zaune a yankin da ke gundumar Kidandan a karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna.
Aminiya ta ziyarci kauyen domin jin yadda lamarin ya faru, sai dai mutanen da wakilinmu ya tattauna da su sun ki yarda a nadi muryarsu ko a dauki hotunansu saboda gudun kada barayin su yi huce a kansu.
Sun bayyana wa Aminiya cewa sama da shekara uku da suka wuce suke cikin ukubar barayin shanun, musamman a kauyukan Karau-Karau da Sako da Iyatawa da Baburu da Galadimawa da Tumburku da Sabon Sara da Sabon Layi da Kidandan da Dogon-Dawa, inda shekara biyu da suka aka kashe mutum talatin suna Sallar Asuba a Dogon-Dawa, kuma sun ce har zuwa yau ba su sake zaman lafiya ba a kauyukan.
Sun ce suna zargin wani da ake hada kai da shi mai suna Alhaji Kundu ne da sace musu mutane da shanu, inda suka ce an ga wasu sun koro shanu sama da 500 da ake zargin na sata ne, kuma da masu neman shanun suka biyo sawu suka ga shanunsu a cikin garken da aka koro, suke zargin hakan ya tunzura shi, “Ya yi mana bi-ta-da-kulli yake kashe mana mutane kuma ya kama wasu daga ciki ya yi garkuwa da su,” inji su.
Sun kara da cewa suna zaton wadannan mutane kamar sun fi karfin hukuma ne domin sun dade suna cin karensu ba babbaka a kansu, sun yi kira ga gwamnati ta dube su da idon rahama ta magance matsalolin karkashe su da ake yi da kuma sace musu shanu.
Da wakilimu ya kira Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna DSP Zubairu Abubakar domin nema karin bayani, sai ya ce zai kira shi, kuma wakilin namu ya sake kiransa har sau uku amma bai dauki waya ba.