Masu sauya sheka dubu 4 sun yi batan dabo a Birnin Kudu

Wani rahoto da jaridar Premium Times da ake bugawa a Intanet ya ce wadansu magoya bayan Jam’iyyar PDP dubu 4 a karamar Hukumar Birnin Kudu, sun yi batan dabo, a lokacin da Gwamna Abubakar Badaru na Jihar Jigawa, ya je can domin karbarsu zuwa Jam’iyyar APC, inda aka neme su kasa ko sama aka rasa. […]

Masu sauya sheka dubu 4 sun yi batan dabo a Birnin Kudu


Wani rahoto da jaridar Premium Times da ake bugawa a Intanet ya ce wadansu magoya bayan Jam’iyyar PDP dubu 4 a karamar Hukumar Birnin Kudu, sun yi batan dabo, a lokacin da Gwamna Abubakar Badaru na Jihar Jigawa, ya je can domin karbarsu zuwa Jam’iyyar APC, inda aka neme su kasa ko sama aka rasa.

A ranar Lahadin da ta gabata ce Gwamna Badaru ya je Birnin Kudu da niyyar karbar wadanda suka canja shekar da kuma kaddamar da ayyukan raya kasa da dan Majalisa mai wakiltar Birnin Kudu da Buji, Honorabu Magaji Da’u Aliyu ya yi, tare da bayar da gudunmawar motoci ga magoya baya. 

Sai kuma kaddamar da aikin gina titi, kuma da ba da takardar cakin kudi na Naira miliyan 20 ga daliban karamar hukumar da ke karatu a makarantun gaba da sakandare.

To amma a yayin da aka kira wanda zai yi jawabi a madadin wadanda suka yi canjin shekar, sai aka rasa shi, babu shi kuma babu sauran mutum dubu 4 da aka ce suna tare da shi. Wannan abu bai yi wa Gwamna dadi ba, inda ya gaggauta gabatar da na sa jawabi a takaice ya bar wurin, inji jaridar. Haka kuma Shugaban taro Honorabul Da’u Aliyu bai yi wa manema labarai jawabin komai ba.