Masu sayar da ruwa suna gallaza wa jama’a a Jigawa
Masu sayar da ruwan leda da aka fi sani da fiya-wata a Jihar Jigawa sun fara gallaza wa jama’ar jihar bayan da dillalan ruwan suka yi musu karin Naira 10 a kan kowace ledar ruwan.Masu sayar da fiya-wata din sun kara farashinsa a Dutse fadar jihar lamarin da ya sa jama’a da dama komawa ga […]
Masu sayar da ruwan leda da aka fi sani da fiya-wata a Jihar Jigawa sun fara gallaza wa jama’ar jihar bayan da dillalan ruwan suka yi musu karin Naira 10 a kan kowace ledar ruwan.
Masu sayar da fiya-wata din sun kara farashinsa a Dutse fadar jihar lamarin da ya sa jama’a da dama komawa ga shan ruwan famfo da na rijiya kuma suke ci gaba da korafi a kan hakan.
A baya dillalan ruwan suna sayar da kowace kunshin ledar ruwan mai cin kananan ledoji 20 a kan Naira 50 ne sai suka mayar da ita Naira 60 saboda kukan da suka yi na samu karin kudin ledar da suke zuba ruwan, amma sai masu sayar da ruwan suka koma sayar da kowace ledar ruwan a kan Naira bakwai wasu ma Naira 10, duk da cewa idan suka sayar a kan Naira biyar-biyar za su samu ribar Naira 40 a kowane kunshin daya.
Wakilimmu ya tuntubi Sakataren kungiyar Masu Yin Ruwa ta Jihar Jigawa Malam Umar Babayaro kan lamarin, inda ya ce ba su kara farashin ruwa ba ga masu sha ba, sai dai sun kara wa dillalai ne saboda tashin farashin ledar da suke zuba ruwan wadda a baya suna sayenta a kan Naira dubu 60 ne amma yanzu ta kai Naira dubu 80. Ya ce wannan karin bai kamata ya shafi masu sayen kwaya-kwayar ledar ruwan don sha ba.
Ya ce sun kafa wani kwamatin ladabtarwa a kan masu sayar da ruwan da suka kara kudin ruwan ga jama’a kuma duk wanda kwamatin ya samu da laifi za su hukunta shi a kungiyance.
Ya shawarci Gwamnatin Tarayya ta shigo kayan yin ledoji kuma ta dauki mataki a kan kamfanonin sarrafa leda don su rage farashin ledojin don saukaka wa talakawa.