Masu sayar da shanu 15 sun rasu a hadarin mota a Kebbi
Mutum 15 masu sayar da shanu sun rasu a wani hadarin mota tirela da ya faru a hanyar Koko zuwa Maiyama a jihar Kebbi. Rahotannin dai na bayyana cewa, masu sayar da shanun sun rasu ne lokacin da suke a hanyarsu na zuwa jihar Legas da Ibadan don sayar da dabbobinsu. Wadanda suka rasun ‘yan […]
Mutum 15 masu sayar da shanu sun rasu a wani hadarin mota tirela da ya faru a hanyar Koko zuwa Maiyama a jihar Kebbi.
Rahotannin dai na bayyana cewa, masu sayar da shanun sun rasu ne lokacin da suke a hanyarsu na zuwa jihar Legas da Ibadan don sayar da dabbobinsu.
Wadanda suka rasun ‘yan garuruwan Andare, Katenga da Maiyama duk a jihar Kebbi.
Wani ganau ya ce, masu sayar da shanun sun dauko sama da shanu 200 lokacin da hadarin ya faru.