Masu sha’awar sarautar Ooni na Ife sun fara bayyana

Bayan an yi jana’izar marigayi Ooni na Ife, Oba Okunade Sijuwade, wanda aka binne shi a cikin harabar fadar masarautar Ife kamar yadda ake binne sarakunan baya, Yanzu haka wasu masu sha’awar hayewa bisa karagar sarautar Ife, sun fara bayyana kansu. Ya zuwa yanzu akwai wasu fitattun mutane guda 6 da suka fara yin kamun […]

Masu sha’awar sarautar Ooni na Ife sun fara bayyana
Masu sha’awar sarautar Ooni na Ife sun fara bayyana

Bayan an yi jana’izar marigayi Ooni na Ife, Oba Okunade Sijuwade, wanda aka binne shi a cikin harabar fadar masarautar Ife kamar yadda ake binne sarakunan baya,
Yanzu haka wasu masu sha’awar hayewa bisa karagar sarautar Ife, sun fara bayyana kansu. Ya zuwa yanzu akwai wasu fitattun mutane guda 6 da suka fara yin kamun kafa ga masu zaben sabon Sarki domin a zabe su a matsayin sabon Ooni da zai gaji marigayi Oba Okunade Sijuwade.
Wadannan mutane 6 sun fito ne daga gidajen sarautu 4 da aka saba zabar daya daga cikin ‘yan takarar da ya cancanci hawa bisa karaga. Gidajen sarautun guda 4 sun hada da Ogboru da Osinkola da Giesi da Lafogido.
Marigayi Oba Okunade Sijuwade ya fito ne daga gidan sarautar Ogboru a yayin da marigayi Oba Adesoji Aderemi, da yayi mulki kafin Oba Okunade ya fito daga gidan sarautar Osinkola. Hakan ya karfafa guiwar ‘yan takara daga gidajen sarautu na Giesi da Lafogido wajen fafutukar ganin daya daga cikinsu ya tsallake siradi domin zama sabon Ooni na Ife.
Mutane 6 da suka fara bayyana sun hada da Dakta Rahman Adegoke Adedoyin da Yarima Yomi Ogunsi da Yarima Eludoyin da Alhaji Sikiru Ayedun da Yarima Adedamola Aderemi da Yarima Adeyeye Enitan Ogunwusi da kowannensu yake ganin shi ne ya cancanci hayewa bisa wannan karaga da ake ikirarin cewa, ita ce tushen yarbawa.
Wakilinmu ya tuntubi Sarkin Hausawan Ile-Ife, Alhaji Mahmuda Abubakar Madagali, game da irin rawar da marigayi Ooni Oba Okunade Sijuwade ya taka a kan al’amuran da suka shafi al’ummar hausawa a zamaninsa.
Madagali ya ce “mun yi babban rashi domin ba za mu taba mantawa da irin gudunmawar da marigayi Ooni na Ife, Oba Okunade Sijuwade, ya bayar ba wajen ci gaban dukkan dan Arewa dake zaune a jihar Osun ba. Wallahi dukkan dan Arewa dake zaune a Jihar Osun, ya ci moriyar mulkin wannan Sarki. Mutum ne mai kaunar baki wanda a dalilin haka ne yayi nasarar shawo kan matsalar cikin gida a tsakanin al’ummar Ile-Ife da suke kallon al’ummar yarbawan Modakeke a matsayin baki. Ni da kaina na karbo takardar raba gardama daga hannun marigayi shugaban kaksa Sani Abacha, da ya bayar a kawo wa Ooni domin tabbatar da kasancewar Modakeke a cikin karamar hukumar Ife ta gabas. A ranar da na mika wannan takarda ga Oba Okunade Sijuwade, a nan take ya haye saman benen gidansa domin yi wa al’umar da suka taru a fadarsa jawabin murna.
Sarkin Hausawan ya ce marigayi Oba Sijuwade shi ne sarkin da ya jawo al’ummar Hausawa kusa da shi. “Wani abun mamaki a duk lokacin da na jagoranci jama’a ta zuwa gaisuwar ban girma a fadarsa sai ya fara karbar bakuncinmu kafin ya saurari mutanen da suka riga mu zuwa fadar ta sa kuma a duk lokacin da zai yi tafiya zuwa wani sashe na Arewacin kasa, yana kama hannu na mu tafi tare ne. Shekaru 6 da wucewa Oba Okunade Sijuwade, ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya ceto al’ummar Hausawa da wasu ‘yan garin Ile-Ife, suka yi yunkurin korarsu daga unguwar Sabo da muke zaune shekaru fiye da 70 a ciki. Da kanshi ya shigo cikin unguwar Sabo dake cikin garin Ile-Ife, ya ba mu tabbacin cewa, babu wanda ya isa ya kore mu daga wannan unguwa kuma shi ne ya ba mu shawarar cewa, mu shigar da kara zuwa kotu wanda ya taimaka da aljihunsa da lauyoyi. Yanzu haka maganar tana gaban kotu.”
Yace, “marigayi Oba Sijuwade, shi ne Ooni na Ife na farko da ya fara sanya Sarkin Hausawa a cikin karamar majalisarsa da take yin taro a kowace ranar juma’a. Abun da muke fata shi ne samun sabon Sarki da zai maye gurbinsa da kyawawan halaye na janyo baki a kusa da shi