Masu shan taba za su shiga uku a Najeriya

Masu shan taba za su shiga uku a Najeriya, domin Gwamnatin Tarayya ta amince da daurin wata shida a gidan yari ko tarar Naira dubu 50 ga duk wanda ya sha taba a wasu kebantattun wurare a Najeriya. Wannan bayani na kunshe ne a sabuwar dokar hana shan taba ta shekarar 2014 da Majalisar Zartarwa […]

Masu shan taba za su shiga uku a Najeriya

Masu shan taba za su shiga uku a Najeriya, domin Gwamnatin Tarayya ta amince da daurin wata shida a gidan yari ko tarar Naira dubu 50 ga duk wanda ya sha taba a wasu kebantattun wurare a Najeriya.
Wannan bayani na kunshe ne a sabuwar dokar hana shan taba ta shekarar 2014 da Majalisar Zartarwa ta amince da ita a taronta na shekaranjiya Laraba.
kudirin dokar ya ce duk kamfanonin da suka saba mata, za a ci su tarar da ta kama daga Naira miliyan daya zuwa miliyan 15, sannan za a daure shugabanin kamfanonin na tsawon shekara daya zuwa biyu.
Ministan Lafiya, Mista Onyebuchi Chukwu wanda ya yi ’yan jarida karin haske kan dokar, bayan da aka tashi daga taron majalisar, wanda aka gudanar a karkashin Shugaba Goodluck Jonathan, ya ce za a tura kudirin dokar ga majalisar dokoki don amincewa da ita.
“Wuraren da aka kebe sun hada da wurin haduwar jama’a, don muna son muhallinmu ya kansance bai gurbata da hayakin taba ba, ta yadda za mu bayar da kariya ga mutanen da ba sa shan taba. Za kuma a ware wurare a ciki da wajen gidaje a matsayin wuraren da ba a son a rika shan taba,” inji shi.
Ministan ya ce kudirin dokar ya haramta tallar taba da kamfanonin taba ke yi. Kuma dokar na duba yiwuwar a mayar da kashi 50 cikin 100 na bangon kwalayen taba dauke da fadakarwa kan illar da ke tattare da shan taba. Ya ce bincike ya nuna cewa, tun daga shekarar 2008, yawan masu shan taba na karuwa a Najeriya, inda ake samun kananan yara da shekarunsu ya kama daga 13 zuwa 15 suna shan taba.
Manufar wannan doka dai, ita ce a shawo kan cututtukan da ake kamuwa da su sanadin shan taba da suka hada da ciwon zuciya da cutar daji da sarkewar numfashi da ciwon sukari.