Masu shayi sun samu tallafin Naira miliyan 208
Kimanin masu sana’ar shayi 5200 ne suka amfana daga tallafin Naira miliyan dari biyu da takwas da gwmaatin Jihar Kano ta kashe wajen sama musu kayayyakin sana’arsu inda kowane mai shayi ya samu kayayyakin na kwatankwacin Naira dubu 40 . Aminiya ta rawaito cewa kayayyakin da aka raba wa masu shayin sun hada da biredi […]
Kimanin masu sana’ar shayi 5200 ne suka amfana daga tallafin Naira miliyan dari biyu da takwas da gwmaatin Jihar Kano ta kashe wajen sama musu kayayyakin sana’arsu inda kowane mai shayi ya samu kayayyakin na kwatankwacin Naira dubu 40 .
Aminiya ta rawaito cewa kayayyakin da aka raba wa masu shayin sun hada da biredi da mangyda da kwai da madara da bournbita da taliyar ‘yan yara da doguwar taliya da man buluban da leda da sukari da kwanduna da kofuna da farantai.
Da yake raba kayayyakin ga masu sana’ar shayin Gwamann Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi wannan tunani ne don tallafa wa masu shayin yadda za su bunkasa sana’arsu ta shayi “mun ba ku wannan tallafi ne don ku kara bunkasa sana’arku tare da bunkasa harkokin tattalin arzikin Jihar Kano”
Gwmna Ganduje ya nemi masu sana’ar shayin da su yi rajista da kungiyarsu ta masu shayi don ci gaban sana’ar tasu. Ya kumayikira gare su da su riki tsafat a harkar sana’arsu ta hanyar tsafatce kayayyakin da suke amfani da su tare da wanke hannunsu a kyaushe da kuma yin amfani da safar hannu. “kasancewar kuna harkar abinci, akwia bukatar ku ba sha’anin tsafta muhimmanci, ta hanyar wanke kayayyakin da kuke amfani da su tare da yin amfani da safar hannu a koyaushe”
Ahmad Rufa’i Mia shayi ne da ke karamar Hukumar Dala yana daga cikin mutanen da suka amfana daga wannan tallafi ya gode wa Gwamnatin Kano kasancewar a cewarsa tallafin zai habaka kasuwancinsa.
Shi ma Alaramma Mai shayi Beli ya yi alkawarin inganta sana’arsa ta shayi “dama babban abin dake ci min tuwo a kwarya a harkar sana’ar nan shi ne rashin jari, amma da wannan kayayyaki da na samu na tabbata zan kara bunkasa sana’ata tare da inganta ta domin amfanin kaina da kuma sauran jama’a” Inji shi.