‘Masu shigo da shinkafa sun ketara iyakar rangwaman gwamnati’

Hukumar Hana Fasa kwauri ta kasa wato (Custom) ta ce ’yan kasuwar da ke shigo da shinkafa daga kasashen ketare sun ketara iyakar rangwaman da Gwamnatin Tarayya ta yi masu na kashi 20 cikin 100 na kudin harajin da yakamata su biya a shekarar 2014, inda suka shigo da ita fiye da ka’ida.Hukumar ta bayyana […]

‘Masu shigo da shinkafa sun ketara iyakar rangwaman gwamnati’
‘Masu shigo da shinkafa sun ketara iyakar rangwaman gwamnati’

Hukumar Hana Fasa kwauri ta kasa wato (Custom) ta ce ’yan kasuwar da ke shigo da shinkafa daga kasashen ketare sun ketara iyakar rangwaman da Gwamnatin Tarayya ta yi masu na kashi 20 cikin 100 na kudin harajin da yakamata su biya a shekarar 2014, inda suka shigo da ita fiye da ka’ida.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata ta hannun Jami’in Hulda da jama’ar hukumar, Wale Adeniyi, inda ya ce hukumar ta rage harajin da take karba daga daga kashi 60 zuwa 20 cikin 100 saboda amfanin masu zuba jari da sabbin masu sarrafa shinkafar. Kuma ya ce an dauki matakin ne saboda a rage karancinta a kasuwa wanda hakan ke jayo tashin farashi. Sai dai jami’in ya ce galibin masu shigo da shinkafar sun saba wa ka’idojin rangwaman gwamnatin.
Daga karshe ya ce: “Muna umarta duk wadanda suka saba tanade-tanaden da su hanzarta tuntubar hukumar domin a warware lissafin. Kuma za su biya kashi 70 cikin 100 ne na harajin kafin ranar 15 ga watan nan.  Wadanda suka ki yin hakan kuma za a bayyana sunanyansu domin cin su tara,” inji shi.