Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Kwankwaso ya ce waɗanda ke iƙirarin gwamnan ya tsaya da ƙafarsa suna da ɓoyayyiyar manufa.

Masu son Abba ya tsaya da ƙafarsa za su cuce shi – Kwankwaso

Kwankwaso

Jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce masu son Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tsaya da ƙafarsa za su kai shi su baro.

A cewarsa, waɗannan mutanen na ƙoƙarinsa ya yi kuskure don su samu damar cin gajiyar lamarin.

Kwankwaso, ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya yi martani kan zargin da ake masa na na yin kaka-gida a harkar gwamnatin Kano.

Ya ce yana bayar da shawara ne kawai idan gwamnan ya nemi hakan daga wajensa.

“Mutane suna buƙatar su fahimci cewa Kwankwasiyya tafiya ce ba jam’iyyar siyasa ba. An gina ta ne a kan amana.

“Idan wani gwamna ko ɗan majalisa da muka mara wa baya ya gaza, ba shi kaɗai zai sha suka ba, har da tafiyar baki ɗaya,” in ji Kwankwaso.

Ya ƙara da cewa waɗanda ke cewa gwamna ya “tsaya da ƙafarsa” suna da wata ɓoyayyar manufa.

“Wasu suna ganin ya tsaya da ƙafarsa yana nufin rabuwa da Kwankwasiyya. A cikinsu akwai waɗanda ke da burin zama gwamna.

“Suna jiran ya yi kuskure don su yi amfani da wannan wajen cin gajiyar lamarin. Ina gode wa gwamnan da ya yi watsi da su,” in ji shi.